Dakarun Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Bindiga, an Kashe Miyagu kusan 100 a Kebbi
- Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka 'yan bindiga masu tarin yawa a jihar Kebbi da ke yankin Arewa maso Yamma
- Sojojin sun samu nasarar ne bayan sun yi kazamin artabu da 'yan bindigan wadanda suka yi niyyar kutsowa cikin jihar
- Nasarar ta zo baya ne sojojin sun samu bayanan sirri kan shirin 'yan bindigan na kawo har-hare
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kebbi - Sojojin da ke gudanar da aikin tsaro a Kebbi sun kashe ’yan bindiga fiye da 80 da suka yi yunkurin shigowa jihar daga iyakar Zamfara.
Sojojin sun samu nasarar ne a wani farmaki da aka bayyana a matsayin babban nasara wajen hana ta’addanci a yankin.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta ce hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai ba gwamna shawara kan harkokin sadarwa da tsare-tsare, Abdullahi Idris Zuru, ya fitar a ranar Lahadi, 26 ga watan Oktoban 2025.

Kara karanta wannan
Babu dadin ji: An tsinci gawar soja a wani irin yanayi bayan bin 'dan bindiga' cikin daji
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun kashe 'yan bindiga a Kebbi
Ya bayyana cewa nasarar aikin na cikin kokarin gwamnatin Kebbi na karfafa tsaro a yankunan da ke kan iyaka.
A cewar Abdullahi Idris Zuru, aikin ya gudana ne a karamar hukumar Ngaski, bayan tura dakarun sojoji da aka horas da kayan zamani a yankunan iyaka da Sokoto, Zamfara da Neja, kamar yadda Gwamna Nasir Idris ya umarta.
“Gwamna Idris ya roki karin dakarun sojoji domin tunkarar matsalolin tsaro a jihar, abin da ya kai ga gudanar da jerin hare-haren da suka hana kungiyoyin ’yan bindiga samun damar kutsawa cikin jihar."
- Abdullahi Idris Zuru
Abdullahi Idris Zuru ya ce bayanan sirri masu inganci ne suka taimaka wajen kai dakarun a kauyen Makurdi, inda aka yi artabu da ’yan bindiga masu dauke da muggan makamai da ke kokarin shiga daga jihar Neja tsakanin daren Juma’a da ranar Asabar.
Daraktan tsaro na jihar Kebbi, Abdulrahman Usman, ya tabbatar da cewa fiye da ’yan bindiga 80 aka kashe, sannan an kwato babura da dama tare da ceto mutane biyu da aka sace.
Sanarwar ta kara da cewa hadin kai tsakanin gwamnatin jihar da hukumomin tsaro, musamman rundunar sojin Najeriya, ya taka muhimmiyar rawa wajen wannan nasara.
An bayyana cewa Gwamna Nasir Idris ya samar da motoci 100 na Hilux da babura 5,000 domin karfafa motsin dakarun tsaro da inganta saurin amsa kiraye-kirayen gaggawa.

Source: Original
Sarkin Yauri ya yaba da nasarar sojoji
A nasa martanin, mai martaba Sarkin Yauri, Dr. Zayyanu Muhammad, ya yaba wa dakarun tsaro bisa jajircewarsu da kuma Gwamna Nasir Idris bisa ci gaba da nuna kishin kare rayuka da dukiyoyin jama’a a jihar.
“Wannan nasara ta nuna cewa hadin kai tsakanin gwamnati da jami’an tsaro yana da muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya."
- Dr. Zayyanu Muhammad
Sojoji sun yi kokari
Legit Hausa ta tuntubi wani mazaunin Kebbi, Lukman Isa Kamba ya yabawa dakarun sojojin kan nasarar da suka samu a kan 'yan bindigan.
"Gaskiya sojoji sun yi kokari kuma muna matukar yaba musu bisa wannan nasarar da suka samu a kan 'yan bindiga."
"Muna rokon Allah ya ci gaba da ba su nasara kan wadannan miyagun."
- Lukman Isah Kamba
Sojoji sun cafke rikakken dan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar cafke wani rikakken dan bindiga a jihar Plateau.
Sojojin sun samu nasarar cafke fitaccen jagoran ‘yan ta’adda, Idris Idris, wanda aka fi sani da Babawo Badoo.
Majiya daga bangaren sojoji ta bayyana cewa Babawo Badoo ya shahara wajen kai hare-hare da sace mutane a yankin Arewa ta Tsakiya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

