Hisbah Ta Soke Shirin Auren Mai Wushirya da 'Yar Guda, an Ji Dalili
- Batun auren Ashiru Idris da Basira 'Yar Guda wanda kotu ta bada umarnin a aiwatar, ya samu koma baya
- Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta sanar da cewa ta soke shirin auren na shahararrun 'yan TikTok wadanda suka yi fice kan irin soyayyar da suke nunawa juna a dandalin
- Ta bayyana cewa ta dauki matakin ne bayan ta gano cewa dama tun da farko ba da zuciya daya suka amince da batun auren ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta tabbatar da soke shirin auren da aka tsara tsakanin shahararrun masu TikTok, Ashiru Idris wanda aka fi sani da Mai Wushirya da Basira Yar Guda Daya.
Soke shirye-shiryen dai na zuwa ne duk da umarnin da wata kotun majistare ta bayar a baya cewa a shirya musu aure cikin kwanaki 60.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta ce mataimakin shugaban hukumar Hisbah, Dr. Mujahideen Aminuddeen Abubakar, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa Hisbah ta soke shirin auren?
Dr. Mujahideen ya ce hukumar ta janye shirin auren ne bayan ta gano cewa ba a samu cikakkiyar yardar juna tsakanin bangarorin biyu ba.
Ya yi bayanin cewa bayan bincike da tattaunawa da bangarorin biyu, hukumar ta gano cewa sun yi kokarin amfani da batun auren ne domin kaucewa hukunci kan zargin badala da ake tuhumarsu da shi a kotu.
“A zaman kotu da ya gabata, bangarorin biyu sun ce suna soyayya ne kuma suna son aure, shi ya sa kotu ta umurce mu da mu taimaka wajen shirya auren."
"Amma da muka fara shirin aure tare da kai su yin gwajin lafiya, dukkansu sun amsa cewa sun yi wannan ikirarin ne saboda tsoron hukuncin da kotu za ta yanke, ba don soyayya ta gaskiya ba."
- Dr Mujahideen Aminuddeen Abubakar
Soyayyar wasa Mai Wushirya da 'Yar Guda ke yi
Ya kara da cewa hukumar ta gano cewa irin nuni da soyayya da suke yi a bainar jama’a a dandalin TikTok wasan kwaikwayo ne da suka tsara domin samun daukaka a kafafen sada zumunta, rahoton The Guardian ya tabbatar da hakan.
Dr. Mujahideen ya ce hukumar ta dauki matakin soke shirin auren gaba daya, domin kauce wa rikici da rashin fahimtar juna a nan gaba, tare da tabbatar da cewa duk wata dangantaka da za ta wanzu tsakaninsu ta kasance bisa yarda da fahimtar juna.
“Mun yanke shawarar dakatar da shirin auren domin kada a tura mutane biyu cikin aure ba tare da yardar juna ba. Auren dole ba zai haifar da zaman lafiya ba."
- Dr Mujahideen Aminuddeen Abubakar

Source: Facebook
Za a maida Wushirya da 'Yar guda kotu
Hukumar Hisbah ta ce ta mika batun komawa kotu domin ci gaba da daukar matakan shari’a da suka dace.

Kara karanta wannan
Babu dadin ji: An tsinci gawar soja a wani irin yanayi bayan bin 'dan bindiga' cikin daji
Tun da farko dai, kotun majistare ta ba da umarni cewa hukumar Hisbah ta shirya auren cikin kwanaki 60 bayan Mai Wushirya da Basira Yar Guda sun bayyana cewa suna son yin aure domin gyara halayensu.
Mai Wushirya ya fasa auren 'Yar Guda
A wani labarin kuma, kun ji cewa shahararren dan TikTok, Ashiru Idris wanda aka fi sani da Mai Wushirya, ya fasa auren Basira 'Yar Guda.
Ashiru Idris ya bayyana cewa dama tun da farko ya amince da batun auren ne saboda tsoron hukuncin da za a yi masa a kotu.
Hakazalika, Mai Wushirya ya nesanta kansa da batun kudin gudunmawa da wasu ke karba don bikin aurensa da 'Yar Guda.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

