An Gano Daloli, Motoci da Alfarma da Tinubu Ya Ware Wa Korarrun Hafsoshin Tsaro
- Sababbin sharuɗɗan murabus na sojoji sun bayyana cewa tsofaffin manyan hafsoshin tsaron ƙasa za su samu manyan motoci da daloli
- Gwamnatin tarayya za ta kashe kuɗi mai yawa wajen kula da waɗanda suka yi ritaya daga rundunar soji, bayan cire hafsoshin tsaro
- Haka kuma, za su ci gaba da amfani da kayan sojoji yayin tarurruka na musamman da samun kariyar lafiya kyauta a gida da kasashen waje
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsofaffin hafsoshin tsaro uku da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cire daga mukamansu jiya za su koma gida da abubuwan alheri.
An tabbatar da cewa za su samu manyan motoci masu sulke guda biyu da kuma motar alfarma kirar 'Prado Jeep', ko makamantan su.

Source: Twitter
Motoci, kudi da korarrun sojoji za su samu
Bugu da ƙari, kowannen su zai karɓi dalar Amurka $20,000 a shekara don kuɗin jinya, kamar yadda kwafin takardar da jaridar Leadership ta gani ya nuna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akalla dalar Amurka 20,000 idan aka juya zuwa kudin Najeriya ya kai kimanin N30m wanda za su samu domin kula da lafiyarsu.
A cewar sabon tsarin yanayin aiki (HTACOS) 2024 da Shugaba Tinubu ya sanya wa hannu, rundunar za ta kula da waɗannan motocin tare da maye gurbinsu duk bayan shekaru huɗu.
Takardar ta bayyana cewa tsofaffin janar-janar da sauran manyan hafsoshin za su sami fa’idodi da dama bayan sun bar aiki, ciki har da kayan sojoji, masu aiki a gida, da kariyar lafiya.

Source: Facebook
Nawa sojojin za su ci moriya bayan ritaya?
A cewar takardar, hafsan tsaro da sauran shugabannin runduna za su samu mota mai sulke da mai kirar Prado, masu aikin gida biyar, direbobi uku, jami’in tsaro ɗaya da kuma masu gadin soja tara.
Haka kuma, za su ci gaba da amfani da kayan sojojin yayin tarurruka na musamman, tare da samun kariyar lafiya kyauta a gida da kasashen waje.
Ga janar-janar masu darajar Laftanar-janar, tsarin ya tanadi motoci biyu, Hilux da Land Cruiser da masu aiki shida da kuɗin jinya har zuwa $20,000 duk shekara.
Ga Manjo-janar da Birgediya-janar, za su samu motar Land Cruiser, masu aiki huɗu da kuɗin jinya $15,000, yayin da wasu manya a cikin za su karɓi motar Toyota Camry da kuɗin jinya $10,000 a shekara.
Rahoton ya ƙara da cewa cire hafsoshin tsaro zai jawo murabus din dole da wadanda lokacinsu ya yi a cikin rundunar, musamman daga janar-janar da ke da daidaiton daraja da wadanda aka sauke.
Mai bincike ya fadi dalilin korar hafsoshin tsaro
Kun ji cewa tun bayan matakin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dauka na sauya manyan hafsoshin tsaro aka fara ce-ce-ku-ce kan dalilan hakan.
Wasu na ganin hakan na da alaka da jita-jitar da aka yada kwanakin baya cewa an kama wasu sojoji na yunkurin juyin mulki.
Sai dai wani babban mai bincike, Oyewole Oginni, ya musanta jita-jitar da mutane ke yadawa, ya ce Tinubu ya yi abin da ya dace a kan lokaci.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

