‘Su Suka Zagaye Shi’: Gwamna Ya Tona Yadda ’Yan Siyasa Suka Munafurci Buhari
- Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kewaye kansa da masu kwaɗayi
- Sule ya bayyana yadda wasu ’yan siyasa ke yaba wa shugabanni yayin da suke mulki, amma suna juya baya da zarar sun bar ofis
- Ya kuma yaba wa marigayi Raymond Dokpesi saboda jarumtar sa wajen kafa gidan rediyo da talabijin na farko mai zaman kansa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana yadda marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya hadu da munafukai.
Abdullahi Sule ya ce Muhammadu Buhari ya kewaye kansa da masu kwaɗayi lokacin da yake mulki wanda suke zuga shi ba don Allah ba.

Source: Facebook
Rahoton Punch ya ce Gwamnan ya bayyana hakan ne a taron tattaunawa da cibiyar “Raymond Dokpesi” ta shirya a Abuja.
'Yadda yan siyasa suka munafurci Buhari'
Sule ya ce ya shaida da idonsa yadda ’yan siyasa ke yaba wa Buhari a ofis, amma suka watsar da shi bayan ya sauka daga mulki.
Ya ce:
“A matsayin Gwamna, na ga yadda kwaɗayi ke lalata zama na gaskiya. Ana cewa Buhari ya fi kowa, amma yanzu ana sukarsa.”
Gwamnan ya kara da cewa, bayan Buhari ya bar mulki, wadannan mutane da suka yaba masa su ne ke cewa shi ne mafi raunin shugaba a tarihi.
Gwamna ya yaba marigayi Dokpesi kan jijircewarsa
Sule, wanda aka karrama da lambar yabo ta NIPR, ya ce yana girmama marigayi Dokpesi saboda jarumtar sa wajen kafa gidan talabijin a lokacin soja.
Ya ce, Dokpesi ya kafa tashar rediyo da talabijin mai zaman kanta a wani lokaci da gwamnati ke da iko a kan yawancin kafafen watsa labarai.
“Ina taya murna da marigayi Dokpesi wanda bai taɓa tsoron faɗa wa gwamnati gaskiya ba, ko da a lokutan wahala.”
- Gwamna Abdullahi Sule

Source: Facebook
An yabawa Gwamna Sule kan kyautar fili
Shugaban NIPR, Dakta Ike Neliaku, ya gode wa Gwamna Sule saboda ba hukumar fili domin gina jami’ar hulɗa da jama’a ta duniya a jihar Nasarawa.
Neliaku ya bayyana cewa aikin ginin jami’ar ya kai matakin cigaba sosai, inda za ta zama cibiyar horas da shugabanni masu hangen nesa.
A cewarsa, jami’ar za ta zama cibiyar koyar da dabarun sadarwa mai inganci da haɗa manufofi da aikace-aikace a Najeriya, cewar Daily Post.
Taron, wanda aka shirya domin girmama marigayi Dokpesi, ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, masana harkokin yada labarai da kwararrun masu hulɗa da jama’a.
Gwamna ya fadi dalilin gwamnoni na shiga APC
Kun ji cewa Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya yi tsokaci kan sauya shekar da wasu gwamnoni da wasu 'yan siyasa ke yi zuwa jam'iyyar APC.
Abdullahi Sule ya bayyana cewa sauya shekar da ake gani daga wajen gwamnonin da fitattun 'yan siyasa, na faruwa ne saboda manufofin Bola Tinubu.
Gwamnan ya bayyana cewa manufofin da gwamnatin shugaban kasan ke aiwatarwa na bukatar matukar jarumta.
Asali: Legit.ng


