Ta Faru Ta Kare: Majalisa Ta Amince da Kirkirar Karin Jiha 1 a Najeriya
- Kwamitin majalisar tarayya na hadin guiwa kan gyaran kundin tsarin mulki ya amince da kafa sabuwar jiha a Najeriya
- An cimma matsayar ne yayin taron kwanaki biyu a Legas, inda aka tattauna kan bukatun kafa sababbin jihohi 55 a fadin kasa
- Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, ya bukaci ‘yan majalisa su marawa kudirin baya domin tabbatar da adalci
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Kwamitin hadin gwiwa na majalisar dattawa da wakilai kan gyaran kundin tsarin mulki ya amince da kafa sabuwar jiha.
Kwamitin ya amince da hakan ne kan kirkirar sabuwar jihar a yankin Kudu maso Gabas domin tabbatar da adalci da daidaito.

Source: Twitter
Za a karawa yanki 1 jiha a Najeriya
An cimma matsayar ne a taron kwanaki biyu da aka gudanar a Legas, inda aka duba bukatu 55 na neman sababbin jihohi, cewar Vanguard.
Wannan mataki zai karawa yankin jiha daya, wanda zai zama jihohi shida gaba daya, domin daidaitawa da sauran yankuna na kasar.
A halin yanzu, yankin Kudu maso Gabas yana da jihohi biyar kacal, wanda ya gaza adadin da ke cikin sauran yankuna na Najeriya.

Source: Facebook
Waye ya jagoranci kwamitin kirkirar sabuwar jiha?
Taron da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya jagoranta, ya tattauna sosai kan bukatar kafa karin jiha.
Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu, wanda ya jima yana fafutukar batun, ya ce bukatar tana da tushe a adalci da daidaito.
‘Yan kwamitin sun amince da bukatar kafa sabuwar jiha a yankin bayan tattaunawa mai zurfi da shawarwari tsakanin membobin majalisar.
Sanata Abdul Ningi daga Bauchi ta Tsakiya ne ya gabatar da kudirin, yayin da Ibrahim Isiaka daga Ogun ya mara masa baya a majalisar.
Goyon baya da kudirin ke samu a majalisa
Kudirin ya samu cikakken goyon bayan mambobin kwamitin, wanda hakan ya tabbatar da amincewa da kafa sabuwar jiha a yankin.
Bayan haka, kwamitin ya kafa wani karamin kwamitin domin duba bukatun kafa sababbin jihohi da kananan hukumomi a fadin kasa.
An bayyana cewa kwamitin ya karɓi sama da bukatu 278 daga sassa daban-daban na kasar domin duba yiwuwar kafa sababbin yankuna.
Sanata Barau Jibrin ya bukaci ‘yan majalisa da na jihohi su hada kai don tabbatar da nasarar wannan kuduri yayin kada kuri’u, Punch ta tabbatar da rahoton.
Ya ce dole ne a samu hadin kan dukkan bangarori na gwamnati domin cimma burin kafa karin jihohi cikin tsarin adalci da gaskiya.
“Dole mu ƙarfafa abin da muka fara domin dukkan sassan ƙasar su shiga cikin wannan tsari.”
- Sanata Barau Jibrin
Majalisa ta fara bitar kirkirar jihohi 55
Mun ba ku labarin cewa Majalisar dattawa ta tabbatar da aniyar yin gyare-gyaren da za su amfanar da al’umma a kundin tsarin mulki na 1999.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya bayyana matakan da ake dauka a halin yanzu.
A taron bitar kwana biyu da aka gudanar a Legas, an tattauna kan bukatun kirkirar jihohi, gundumomi da sauransu domin inganta shugabanci.
Asali: Legit.ng

