Daliban Katsina Za Su Warwasa, Gwamna Ya Fitar da Sama da Naira Miliyan 600 na Tallafin Karatu
- Gwamnan Katsina ya waiwayi daliban jihar da ke karatu a makarantun gaba da sakandire daban-daban a fadin Najeriya
- Malam Dikko Radda ya fitar da kudi sama da Naira miliyan 677 domin bai wa daliban tallafin karatu na zangon 2024/2025
- Gwamnatin Katsina ta ce wannan mataki ya kara nuna yadda Gwamna Dikko Radda ya dauki fannin ilimi da muhimmanci
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina, Najeriya – Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda, ya amince da sakin ₦677,572,815 domin biyan kudin tallafin karatu ga dalibai yan asalin jihar.
Wadannan kudi da gwamnan ya fitar sun kunshi tallafin karatun da ake ba dalibai duk shekara, kyautar daliban da suka nuna hazaka da tallafin musamman ga dalibai masu nakasa.

Source: Facebook
Mai magana da yawun gwamnan Katsina, Ibrahima Kaulaha Mohammed ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna ya tallafa wa daliban Katsina
Ya ce za a raba tallafin ne ga daliban da ke karatu a jami'o'i da manyan makaratun gaba da sakandire daban-daban a fadin Najeriya.
Da wannan mataki, jarin da gwamnatin Katsina ta zuba a fannin tallafin dalibai ya kai jimillar Naira biliyan 2.6.
Tallafin dai ya amfani dubban ɗalibai kai tsaye, tare da ƙara tabbatar da matsayar gwamnatin Katsina wajen ci gaban ilimi a Arewacin Najeriya.
Yadda za a raba kudin ga daliban Katsina
Sanarwar ta ce:
"Daga cikin kudin da aka fitar, za a raba ₦283,521,639 a matsayin tallafin karatu ga sababbin ɗalibai da suka shiga jami’o’i, kwalejoji da makarantun gaba da sakandare yan asalin Katsina a fadin ƙasar nan."
"Naira miliyan 15 kuma za a yi amfani da su wajen kyautar karramawa ga daliban da suka kammala karatu da sakamako mafi girma (First Class) a fannoni daban-daban.
"Haka kuma, an ware Naira miliyan 7 domin shirin tallafin karatu na musamman ga dalibai masu bukata ta musamman."
Wannan na zuwa ne bayan gwamnan Katsina ya saki ₦372,051,176 a watan Satumba 2024 domin biyan tallafi ga daliban da ke ci gaba da karatu.
Hakan ya kai jimillar kudaden da aka fitar a zangon karatu na 2024/2025 zuwa ₦677,572,815.

Source: Facebook
Gwamna Dikko na kokarin inganta ilimi
Sanarwar ta ce wannan mataki na nuna jajircewar Gwamna Radda wajen ganin ilimi ya zama ginshiƙin ci gaba, bunƙasa tattalin arziki da haɗa kan al’umma, a karkashin manufarsa ta “Building Your Future Agenda."
Kakakin gwmanan ya ƙara da cewa tun lokacin da Dikko Radda ya hau mulki, ya bai wa ilimi muhimmanci ta hanyar zuba jari mai yawa a shirye-shiryen tallafin karatu.
Wani dalibin jami'a ya yabawa Dikko Radda bisa yadda yake kokari wajen taimaka wa yan asalin jihar Katsina su samu ilimi.
Kabir Sulaiman, wanda ke karatu a Jami'ar Tarayya ta Gusau ya shaidawa Legit Hausa cewa tallafin gwamnatin Katsina da bashin gwamnatin Tinubu sun ceci karatun talakawa irinsa da yawa.

Kara karanta wannan
Akwai yiwuwar mata su karu a majalisa, gwamnoni sun goyi bayan kudiri na musamman
Dalibin ya ce:
"Gwamnan Katsina ya cancanci yabo, tun da ya zo ana samun kudin Scholarship a kan lokaci, kuma musamman mu talakawa yana mana amfani.
"Yanzu karatu ya yi tsada, sai da irin wadannan tallafin muke iya biyan kudin makaranta, tsarin gwamnatin tarayya na bada bashi ya taimaka mana."
Katsina: Gwamna Radda ya yi garambawul
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya yi garambawul gwamnatinsa domin inganta harkokin mulki.
Gwamna Radda ya canza ma’aikatu ga wasu kwamishinoni tare da nada sababbin masu ba shi shawara guda biyu, domin karfafa ingancin aiki a gwamnatinsa.
Mai magana da yawun gwamnan, Ibrahima Kaulaha Mohammed ya tabbatar da hakam tare da jero kwamishinonin da aka sauya wa wurin aiki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

