Ba Sauran Daraja: Sakataren APC Ya Shiga Hannu kan Zargin Kisan Wata Mata

Ba Sauran Daraja: Sakataren APC Ya Shiga Hannu kan Zargin Kisan Wata Mata

  • Ana zargin wani jigo a jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya da kisan kai wanda yan sanda suka fara bincike kansa domin gano gaskiya
  • Rundunar ‘yan sanda a Yobe ta cafke sakataren mazaba na APC a Karasuwa bisa zargin kashe wata mata a Gashuwa da ke jihar
  • Wanda ake zargin ya amsa cewa ya kashe Falmata Abubakar bayan saɓani da suka samu lokacin da take neman taimakon kuɗi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Damaturu, Yobe - Wani daga cikin shugabannin jam'iyyar APC a jihar Yobe ya shiga hannu kan zargin kashe wata mata.

Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta kama sakataren APC na mazaba a Karasuwa bisa zargin kashe wata mata a Gashuwa da ke jihar.

Sakataren APC ya shiga komar yan sanda a Yobe
Kwamishinan yan sanda a jihar Yobe, Emmanuel Ado. Hoto: SP Dungus Abdulkarim.
Source: Facebook

Yobe: Yan sanda sun kama sakataren APC

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Dungus Abdulkarim shi ya tabbatar da haka a ranar 23 ga watan Oktobar 2025 a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: An kama dalibin jami'ar IBB kan saboda gwamna a Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dungus ya bayyana cewa wanda ake zargi Abdulmumini Garba, mai shekara 60, mazaunin Gasma ne.

An kama shi ne bayan da aka gano gawar wata mata mai suna Falmata Abubakar a kusa da Jami’ar Tarayya da ke Gashuwa makon da ya gabata.

Wane martani wanda ake zargin ya yi?

Rahoton ya ce wanda ake zargin yana rike da mukamai biyu a jam’iyyar APC da kasuwar Gwari, wanda hakan ya jawo ce-ce-ku-ce a yankin.

‘Yan sanda sun kama shi ne bayan gudanar da bincike mai zurfi da tattara bayanai a ranar 17 ga watan Oktoba, 2025.

Lokacin da ake masa tambayoyi, Garba ya amsa cewa shi ne ya kashe Falmata Abubakar a cikin motarsa bayan samun saɓani tsakaninsu.

Yan sanda sun kama sakataren APC kan zargin kisan kai
Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe. Hoto: Mamman Mohammed.
Source: Facebook

Yadda matar ta rasa ranta a hannun sakataren APC

An bayyana cewa rikicin ya samo asali ne daga bukatar marigayiyar ta neman taimakon kuɗi don tallafa wa sana’arta, kafin lamarin ya rikide wanda har ya yi sanadin ran matar.

Kara karanta wannan

Injiniyoyi sun ga kokarin Gwamna Abba, sun ba shi lambar girmamawa

Bayan kisan, Garba ya ce ya jefar da gawar marigayiyar a daji da ke kusa da wurin misalin ƙarfe 10 na dare domin rufawa kansa asiri kan kisan da ya yi.

Rundunar ‘yan sanda ta yaba da ƙwarewar jami’anta wajen gano wanda ake zargi cikin gaggawa ta hanyar dabarun tattara bayanai da bincike.

Kwamishinan ‘yan sanda, Emmanuel Ado, ya jinjinawa sashen Bade, yana tabbatar da cewa za a gurfanar da wanda ake zargi bayan an kammala bincike.

Ana zargin basarake, kansila da satar transifoma

Mun ba ku labarin cewa dubun wasu masu girma a cikin al'umma ya cika bayan cafke su da satar tiransifomar wutar lantarki a jihar Gombe.

Rundunar ƴan sanda ta yi nasarar cafke kansila da kuma dagacin kauyensu kan zargin sata da kuma siyar da tiransifoma da aka samar domin al'ummar yankin su amfana.

Kakakin rudunar 'yan sanda a Gombe, ASP Buhari Abdullahi shi ya tabbatar da faruwar lamarin inda a wancan lokaci ya ce suna kan bincike.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.