Jami'ar FUDMA Ta Samu Sabon Shugaba bayan Tantace Farfesohin da ke Takara
- An tantance mutanen da suka nemi kujerar shugabancin jami'ar tarayya da ke Dutsin-ma (FUDMA) a jihar Katsina
- Bayan tantancewa majalisar gudanarwa ta jami'ar FUDMA, ta zabi mutum daya domin jan ragamar shugabancin jamiar
- Majalisar ta amince da nadin Farfesa Mohammed Khalid Othman a matsayin sabon shugaban jami'ar FUDMA
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Majalisar gudanarwa ta jami’ar tarayya Dutsin-ma (FUDMA) da ke jihar Katsina ta tabbatar da nadin sabon shugaban jami'ar.
Majalisar gudanarwar ta tabbatar da nadin Farfesa Mohammed Khalid Othman a matsayin sabon shugaban jami’ar FUDMA.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta ce nadin ya biyo bayan taron musamman karo na 36 na majalisar da aka gudanar a otal din Grand Amber Hotel and Suites, Dutse, jihar Jigawa.
An zabi sabon shugaban jami'ar FUDMA
Tashar Channels tv ta ce shugaban majalisar gudanawar jami'ar FUDMA, Ali Abubakar Jatau, ya bayyana hakan.
Ali Abubakar Jatau ya ce an zabi Farfesa Othman bayan tsarin tantancewa wanda ya kunshi ’yan takara 17 da aka zaba daga cikin 28, da kuma sauran ’yan takara uku da kwamitin bincike ya gano.
“An gayyaci ’yan takara 17 da aka zaba don tantancewa, kuma bayan cikakken tsarin tantancewa mai gaskiya, kwamitin ya gabatar da sunayen mutane uku da suka fi cancanta ga majalisar gudanarwa."
"Majalisar ta amince da nadin Farfesa Mohammed Khalid Othman a matsayin sabon shugaban jami’a."
- Ali Abubakar Jatau
Wanene Farfesa Mohammed Khalid Othman?
An haifi Farfesa Mohammed Khalid Othman a ranar 22 ga Yuli, 1962, a karamar hukumar Bindawa ta jihar Katsina.
Injiniya ne na noma wanda ya yi suna a fannin bincike da shugabanci a harkokin ilimi.
Ya samu digiri na farko, na biyu da na digirgir (Ph.D.) daga Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria (ABU), inda ya taka rawa a fannoni da dama na koyarwa da gudanarwa.

Source: Facebook
Farfesa Othman ya taba rike mukamin shugaban cibiyar nazarin harkokin fadakarwa da hulda da manoma (NAERLS) ta ABU, Zaria, kafin nadin sa a matsayin shugaban jami’a.
Hakazalika mamba ne a majalidar gudanarwa ta jami'ar FUDMA daga bangaren majalisar dattawa ta jami’ar.
Ya na da aure da ’ya’ya tara, kuma ya samu shekaru da dama na gogewa a fannin koyarwa, bincike, da shugabanci.
Majalisar ta bayyana cewa tana da cikakken kwarin guiwa cewa sabon shugaban jami’ar zai kawo sabon hangen nesa da kwarewa wajen ci gaban jami’ar tarayya Dutsin-Ma.
Dalibai sun yi zanga-zanga a FUDMA
A wani labarin kuma, kun ji cewa dalibai a jami'ar tarayya da ke Dutsinma (FUDMA) a jihar Katsina sun gudanar da zanga-zanga.
Daliban sun gudanar da zanga-zangar ne domin nuna fushinsu kan kashe wani dalibi da ake zargin 'yan sa-kai sun yi a yankin.
Wasu bayanai sun nuna cewa an zargi dalibin mai suna Sa'id Abdulkadir da kasancewa mai ba da bayanai ga ‘yan bindiga, yayin da wasu ke cewa an harbe shi ne bisa kuskure yayin da yake tafiya akan babur na haya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

