Sauya Manyan Sojoji zai Iya Jawo Sama da Janar 60 Su Yi Murabus a Najeriya

Sauya Manyan Sojoji zai Iya Jawo Sama da Janar 60 Su Yi Murabus a Najeriya

  • Bola Tinubu ya cire manyan hafsoshin tsaro da suka hada da Janar Christopher Musa, tare da nada sababbi a mukamansu
  • Rahotanni sun nuna cewa sama da Janar 60 za su iya yin murabus saboda sabon tsarin jagoranci a rundunonin soja
  • Fadar shugaban kasa ta ce sauyin na daga cikin matakan karfafa tsaro da inganta daidaito tsakanin rundunonin soja

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Sabon sauyi da aka yi a rundunar sojan Najeriya ya girgiza tsarin tsaro na ƙasa, inda aka cire manyan hafsoshin tsaro tare da nada sababbi a mukaman su.

Sauyin da aka sanar da shi a ranar Juma’a,ya shafi manyan sojojin Najeriya, ciki har da Janar Chiristopher Musa.

Tinubu da sababbin hafsoshin tsaro
Shugaba Tinubu da sababbin hafsoshin tsaro a Abuja. Hoto: Dada Olusegun
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta hada rahoto kan yadda ake hasashen sauyin zai shafi manyan sojojin Najeriya a kwanaki masu zuwa.

Kara karanta wannan

Janar Musa ya bar hafsun tsaro ba tare da cika alkawarin cafko Bello Turji ba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugabannin soja da Tinubu ya nada

A cikin sababbin nade-naden, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, wanda a baya shi ne babban hafsan sojan kasa, yanzu ya zama babban hafsan tsaron ƙasa.

Haka kuma, Manjo Janar Waidi Shaibu ya zama sabon babban hafsan sojan kasa, yayin da Air Vice Marshall Sunday Kelvin Aneke ya karɓi mukamin babban hafsan sojan sama.

Rear Admiral Idi Abbas Idi Abbas ne sabon babban hafsan sojan ruwa, yayin da Manjo Janar E.A.P. Undiendeye ya ci gaba da rike mukaminsa.

Rahotanni sun bayyana cewa za a yi musu karin girma nan ba da jimawa ba, lamarin da zai tilasta manyan hafsoshi da ke gabansu su yi murabus.

Yawan hafsoshin da za su yi murabus

Wata majiyar soja ta tabbatar da cewa sabon tsarin zai shafi jami’ai daga wadanda aka dauka aiki a runduna ta 38, 39, da kuma wasu daga 40 na makarantar sojin Najeriya (NDA).

Kara karanta wannan

ADC ta aika sako mai zafi ga Tinubu kan sauya hafsoshin tsaro

An bayyana cewa hakan yana cikin tsarin soja na tabbatar da bin dokar mukami da kare tsari a tsakanin jami’ai.

Janar Christopher Musa
Tsohon hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Majiyar ta kara da cewa:

“Duk lokacin da aka nada sababbin hafsoshi, dole waɗanda suka fi su girma su bar aiki domin kiyaye tsarin soja.”

Ra’ayin masana kan sauya sojoji

Tsohon kakakin rundunar sojin ƙasa, Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka (mai ritaya) ya bayyana cewa wannan sauyin al’ada ce ta dindindin a tsarin soja.

Ya ce:

“Sauyin jagoranci abu ne da ake yi lokaci zuwa lokaci domin kara ƙwazo da dabaru a ayyukan tsaro.”

Jaridar Punch ta rahoto cewa Manjo Janar Anthony Atolagbe (Mai ritaya) ya bayyana cewa sauyin ba sabon abu ba ne a gidan soja.

Kafin yanzu, Mai girma Bola Tinubu ya canza wasu hafsoshin tsaron a Yulin 2023.

Dalilan sauyin daga fadar shugaban kasa

A wani rahoton, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta bayyana cewa sauyin na cikin kokarin gwamnati na tabbatar da tsaro da inganta hadin kai tsakanin rundunonin soja.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya sa labule da sababbin hafsoshin tsaron Najeriya a Aso Rock

Sanarwar ta bayyana cewa matakin zai taimaka wajen samar da sababbin dabaru a yaki da ta’addanci da sauran ayyukan tsaro a sassan ƙasar.

A wata sanarwa da hadimin shugaban ƙasa, Sunday Dare, ya sanya wa hannu, ya jinjinawa tsofaffin hafsoshin bisa “gaskiya, kishin ƙasa da sadaukarwa” da suka nuna.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng