An Dawo da 'Yan Najeriya 150 da Suka Makale a Kasar Nijar
- Hukumar NEMA ta ce ta karɓi ’yan Najeriya 150 daga Agadez, Jamhuriyar Nijar, bayan makalewarsu a ƙasar
- An saukar da su ne da safiyar Alhamis da misalin ƙarfe 5:20 na safe a filin jirgin saman Malam Aminu Kano
- An ba su kulawa ta gaggawa, abinci da magani, tare da taimakon hukumar IOM da sauran hukumomi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta tabbatar da karɓar ’yan Najeriya 150 da suka makale a Agadez, Jamhuriyar Nijar.
NEMA ta bayyana cewa jirgin da ya ɗauko su ya sauka lafiya a filin jirgin saman Malam Aminu Kano da misalin ƙarfe 5:20 na safe, ranar Alhamis, 23, Oktoba, 2025.

Source: Twitter
Hukumar ta wallafa a X cewa an yi aikin ne tare da haɗin gwiwa tsakanin NEMA, Hukumar kasa ta ’yan gudun hijira (NCFRMI), da kuma kungiyar kasa da kasa mai lura da hijira (IOM).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An dawo da 'yan Najeriya daga Nijar
A cewar sanarwar NEMA, shirin ya kasance wani ɓangare na AVR da IOM ke tallafawa tare da goyon bayan gwamnatin tarayya domin dawo da ’yan Najeriya cikin mutunci.
An bayyana cewa bayan isowarsu, jami’an hukumar shige da fice (NIS) sun gudanar da rijistar bayanan su da daukar hotunan yatsunsu domin tabbatar da sahihancin takardunsu.
Bayan hakan, an tura su zuwa otal ɗin Bizare Luxury a Kano domin tantancewa da samun mafaka na ɗan lokaci ranar 24, Oktoba, 2025.
'Yan Najeriya 150 sun dawo daga Nijar
NEMA ta bayyana cewa cikin mutum 150 da aka dawo da su akwai manya maza 88, mata 32, yara maza 14, da yara mata 16, wanda ke nuna cewa mafi yawansu matasa ne.
An tabbatar da cewa wasu daga cikinsu sun yi watanni suna makale a ƙasar Nijar sakamakon tsadar sufuri da matsalolin tsaro da ke tsakanin ƙasashen yankin Sahel.

Source: Twitter
Hukumar ta ce an shirya musu tsari na musamman don taimaka musu su sake komawa rayuwa cikin jama'a ba tare da wahala ba.
Kulawar da hukumar NEMA ta ba su
NEMA ta bayyana cewa gwamnatin tarayya na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da cewa kowanne ɗan ƙasa da ke waje da ke son dawowa ya dawo cikin aminci da mutunci.
Punch ta wallafa cewa an ba su abinci, ruwan sha, magunguna, da taimakon motocin asibiti ga masu buƙatar kulawar lafiya.
Hukumar ta bayyana cewa nasarar wannan aiki ta samu ne sakamakon haɗin kai tsakanin NEMA, IOM, NCFRMI, da sauran abokan hulɗa.
'Yan gudun hijira: UN ta yabi Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa majalisar dinkin duniya (UN) ta yaba wa gwamnatin Najeriya kan kula da sansanonin 'yan gudun hijira.
Rahoton da majalisar dinkin duniya ta fitar ya nuna cewa ana tallafawa 'yan gudun hijira su samu hanyoyin dogaro da kai a Najeriya.
Hakan na zuwa ne bayan jami'an UN sun gudanar da wani taro na kwana uku a Najeriya tare da kafa cibiyar tattara bayanai a Yobe.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


