'Yan Najeriyan da suka tare a kasashen waje basu da ta cewa kan matsalar kasar

'Yan Najeriyan da suka tare a kasashen waje basu da ta cewa kan matsalar kasar

- Mataimakin majalisar wakilai ta kasa ya soki batun 'yan Najeriya masu korafi daga waje

- Yace, duk dan Najeriyan da ke wata kasa a zaune bai san matsalolin kasar ba, bai da ta cewa

- A fahimtarsa, mazaunin cikin Najeriya shine kadai ke iya fahimtar halin da kasar ke ciki

Mataimakin kakakin majalisar wakilai, Idris Wase ya bayyana cewa 'yan Najeriya mazauna kasashen waje ba su da 'yancin aikawa da korafi ga majalisar kan al'amuran da ke faruwa a Najeriya, The Nation ta ruwaito.

Musamman, ya ce ba su da 'yancin yin korafi game da rashin tsaro tunda ba sa rayuwa a kasar.

Wase, wanda ke wakiltar Mazabar Tarayya ta Wase, ta Jihar Filato, ya fadi hakan ne a zaman da aka yi a ranar Alhamis din da ta gabata yayin zama da Kakakin Majalisar, Femi Gbajabiamila.

Ya ce 'yan Najeriya da ke zaune a kasashen waje ke jin dadinsu ba su da ikon gabatar da koke-koke ga Gwamnatin Tarayya kan batutuwan da suka shafi rashin tsaro.

Ya yi magana ne lokacin da wani dan majalisa, Mark Gbillah, mai wakiltar mazabar Gwer ta Gabashin-Gwer ta Yamma ta Jihar Benue, ya yi kokarin gabatar da wata bukata da kungiyar Mzough U Tiv Amerika (MUTA) ta shigar kan rashin tsaro a Benue, Nasarawa da Taraba.

KU KARANTA: Sarkin Musulmi ya sanar da ranar Litinin 1 ga watan Sha'aban

'Yan Najeriyan da suka tare a kasashen waje basu da ta cewa kan matsalar kasar
'Yan Najeriyan da suka tare a kasashen waje basu da ta cewa kan matsalar kasar Hoto: The Nation
Asali: UGC

Gbillah ya bayyana cewa yana mika bukatar ne a madadin MUTA saboda an kori 'yan asalin jihohin da abin ya shafa daga kasashen kakanninsu.

Kafin ya ci gaba da magana, Wase, wanda yake na jam’iyya mai mulki ta APC, ya ce: “Hon. Gbillah, ka ce Tiv a Amurka? Me suka sani game da Najeriya?

“Menene ya shafesu? Ba za su zauna a can suna jin dadinsu ba kuma su san abin da ke faruwa a Nijeriya.”

Mataimakin Shugaban Majalisar ya ce 'yan Najeriya da ke kasashen waje ba su da 'yancin gabatar da korafi game da rikicin, yana mai cewa za a iya fahimta ne kadai "idan wannan koken ya fito daga wadanda ke cikin kasar."

Gbillah yayi jayayya da cewa yan Najeriya mazauna kasashen waje za su iya gabatar da korafi saboda suna da yan uwa da ke zaune a kasar.

Gbillah ya kuma mayar da martani da cewa Sashi na 40 na kundin tsarin mulki bai hana ‘yan kasa walwala ba.

Gbillah ya yi ikirarin cewa Najeriya ta kasance tana aiwatar da manufar hada kan ‘yan kasarta da ke kasashen waje, manufar da ba za a ci nasara a kanta cikin sauki ba idan ba a ba wa 'yan Najeriya dama su yi magana a kan batutuwan da suka shafi kasar ba.

"Zan tura ka zuwa ga kwamiti kan 'yan Najeriya mazauna kasashen Waje, idan ka bi ta wannan, ba wani abin da ya dace da abin da kake gabatarwa yanzu, ban gamsu da cewa dole ne mu dauki wannan koken ba," in ji Wase.

Bayan haka an yi watsi da koken na Gbillah ba tare da adawa daga wani dan majalisar ba.

KU KARANTA: Dalilin da ya sa na bada shawarin nada Abdurrasheed Bawa shugaban EFCC, Malami

A wani labarin, Majalisar wakilai ta nemi gwamnatin tarayya da ta dauki hayar sojojin kasashen waje domin yakar masu tayar da kayar baya na kungiyar Boko Haram.

Majalisar ta yanke wannan shawara ne sakamakon wani kudiri da Abdulkadir Rahis ya gabatar a ranar Laraba.

Kudirin na Mista Rahis ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sake tsara dabarun yaki da masu tayar da kayar baya.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel