Duniya Labari: Kwamishina Mai Ci a Gombe Ya Yi Bankwana da Duniya

Duniya Labari: Kwamishina Mai Ci a Gombe Ya Yi Bankwana da Duniya

  • Gwamnatin jihar Gombe ta tabbatar da rasuwar Kwamishinanta a yau Juma'a 24 ga watan Oktobar 2025 bayan hatsarin mota
  • Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya nuna jimami kan rashin kwamishinan tsaron cikin gida
  • Marigayi Kanal Abdullahi Bello (mai ritaya), ya rasa ransa ne a wani mummunan hatsarin mota a hanyar Malam Sidi zuwa Gombe

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gombe - Gwamnatin Gombe ta tabbatar da rasuwar Kwamishinanta a jihar wanda ya gamu da mummunan hatsarin mota inda ta yi alhini kan babban rashin da aka yi.

An tabbatar da cewa marigayin wanda shi ne kwamishinan Tsaron Cikin Gida, Kanal Abdullahi Bello (mai ritaya) ya gamu da ajalinsa yayin dawowa jihar Gombe daga Maiduguri.

Kwamishina a Gombe ya rasa ransa bayan hatsarin mota
Gwamna Inuwa Yahaya da kwamishinan tsaron cikin gida, Kanal Abdullahi Bello. Hoto: Ismaila Uba Misilli.
Source: Facebook

An yi rashin kwamishina a Gombe

Hakan na cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan, Ismaila Uba Misilli ya tabbatar a shafinsa na Facebook a daren yau Juma'a 24 ga watan Oktobar 2025.

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya yi garambawul a gwamnatinsa, an sauyawa kwamishinoni ma'aikatu

Sanarwar ta ce hatsarin ya faru ne a kan hanyar Malam Sidi zuwa Gombe, inda ɗan sandansa, Sajan Adamu Husaini, shi ma ya rasa ransa.

Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana rasuwar Kanal Bello a matsayin babban rashi ga gwamnati da al’umma, yana bayyana shi a matsayin jami’i mai kishi.

Abin da Gwamna ya ce kan marigayin

Gwamnan ya ce marigayin ya yi amfani da ƙwarewarsa ta soja wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya wanda Gombe ke alfahari da shi a Najeriya.

"Za a riƙa tunawa da Kanal Abdullahi Bello (Mai Ritaya) a matsayin ginshiƙi wajen tabbatar da ɗa'a, jajircewa da sadaukar da kai, yayin da ya gudanar da ayyukansa cikin himma da sanin ya kamata.
"Rasuwarsa babban rashi ne ba ga iyalansa da gwamnatinmu kaɗai ba, har ma ga Jihar Gombe da Najeriya baki ɗaya."

- Gwamna Inuwa Yahaya cikin alhini

Gwamna ya kadu bayan rashi kwamishina a Gombe
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jigar Gombe. Hoto: Ismaila Uba Misilli.
Source: Facebook

Gudunmawar da marigayin ya bayar a Gombe

Kara karanta wannan

"An kawo El Rufa'i," Obasanjo ya tona abin da ya faru kafin Yar'adua ya zama shugaban kasa a 2007

Inuwa Yahaya ya kuma yaba da gudunmawar marigayin wajen tsara manufofin tsaron cikin gida da haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro don kare lafiyar jama’a.

Gwamnan ya miƙa ta’aziyya ga iyalan marigayin, al’ummar Balanga, da iyalan dogarinsa, yana addu’ar Allah ya gafarta musu, ya kuma saka musu da Aljanna.

Haka zalika ya jajantawa direban da ya jikkata a hatsarin, yana roƙon Allah ya ba shi lafiya da gaggawa daga raunukan da ya samu.

Gwamnatin jihar ta ce za a sanar da lokacin jana’izar marigayin da sauran waɗanda suka rasu daga baya.

Legit Hausa ta tattauna da dan Gombe

Wani daga yankin da marigayin ya fito ya bayyana jimami game da rashin inda ya ce tabbas Kanal Bello mutumin kirki ne.

Aminu Muhammad ya ce Allah bai barin wani don wani, amma mutanen yankin za su yi kewarsa sosai duba alherinsa.

Ya ce:

"Mutum ne mai faraha da taimakon mutane kuma ba shi matsala duk da cewa tsohon soja ne da ya yi ritaya."

Gwamna Inuwa ya jajanta mutuwar tsohon kwamishina

A baya, kun ji cewa, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya tura sakon ta'aziyya bayan babban rashi da jihar ta yi na tsohon kwamshina da ya bayar da gudunmawa sosai.

Kara karanta wannan

Injiniyoyi sun ga kokarin Gwamna Abba, sun ba shi lambar girmamawa

Inuwa ya bayyana rasuwar tsohon kwamishina Julius Ishaya Lepes a matsayin babban rashi ga jihar da al’ummar Kaltungo baki ɗaya.

Gwamnan ya ce Lepes ya bayar da gudunmawa mai tarin amfani ga APC da majalisar zartarwa lokacin da ya rike kujerar kwamishina a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.