Babbar Magana: Shugaba Tinubu Ya Kori Hafsoshin Tsaron Najeriya, Ya Nada Sababbi
- Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya waiwayi shugabannin hukumomin tsaron Najeriya kwanaki kadan bayan jita-jitar an yi yunkurin juyin mulki
- Shugaba Kasa Tinubu ya sauke Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa da sauran hafsoshin rundunar sojojin Najeriya a lokaci guda
- A sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar yau Juma'a, Tinubu ya dauke Janar Olufemi Oluyede daga rundunar sojojin kasa zuwa Hafsan Tsaro
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Najeriya – Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kori Babban Hafsan Tsaro na ƙasa (CDS), Janar Christopher Musa, tare da wasu manyan hafsoshin tsaron Najeriya.

Kara karanta wannan
Tsohon janar ya fadi abin da zai faru a gidan soja bayan Tinubu ya yi sauye sauye
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin yada labarai, Sunday Dare, ya fitar ranar Juma’a, 24 ga watan Oktoba, 2025.

Source: Twitter
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin kafafen sada zumunta, Dada Olusegun ya wallafa sanarwar korar hafsoshin tsaron da kuma nada sababbi a shafinsa na manhajar X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jerin sababbin hafsoshin tsaron Najeriya
A cewar sanarwar, Shugaba Tinubu ya maye gurbin Musa da Janar Olufemi Oluyede, babban hafsan sojojin kasa, ya koma matsayin Babban Hafsan Tsaro na Kasa.
Haka kuma, Manjo Janar W. Shaibu shi ne sabon Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, yayin da Air Vice Marshal S.K. Aneke ya zama sabon Babban Hafsan Sojojin Saman Najeriya.
Bugu da kari, Shugaba Tinubu ya nada Rear Admiral I. Abbas a matsayin sabon Babban Hafsan Rundunar Sojin Ruwan Najeriya.
Sai dai Shugaban Hukumar Leken Asiri na Tsaro Manjo Janar E.A.P Undiendeye, ya tsira daga garambawul din shugavan kasa, zai ci gaba da rike matsayinsa.
Sanarwar ta ce:
“Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi sauye-sauye a tsarin shugabancin rundunonin tsaro domin ƙara ƙarfafa tsarin tsaron ƙasa da inganta tsare-tsaren gwamnati.”
Nasihar da Tinubu ya yi wa hafsoshin tsaro
Bola Tinubu, wanda shi ne Babban Kwamandan Askarawan Najeriya, ya gode wa Janar Christopher Musa da sauran hafsoshin da suka bar aiki bisa kwarewa, kishin ƙasa da sadaukarwa da suka yi a lokacin aikinsu.
Ya kuma bukaci sababbin hafsoshin tsaron da su nuna wa jama'a cewa sun cancanci amincewar da aka nuna gare su, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

Source: Twitter
Bola Tinubu ya bukaci su tabbatar da cancantar su ta hanyar ƙara haɓaka ƙwarewa, faɗakarwa da haɗin kai a cikin rundunonin tsaro, domin inganta tsaron rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa.
Da gaske an yi yunkurin juyin mulki?
A wani labarin, kun ji cewa Hedikwatar Tsaron Ƙasa (DHQ) ta karyata jita-jitar da wasu kafafen labarai suka yada cewa soke bikin cika shekara 65 da samun ‘yancin kai ya samo asali ne daga yunkurin juyin mulki.
A rahotannin da ake yadawa, an ce an kama wasu manyan sojoji har 16 da ake zargin suna da hannu a yunkurin kifar da gwamnatin Tinubu.

Kara karanta wannan
Gwamnan Kogi ya yabi hangen nesan Tinubu da ya nada 'dan jiharsa hafsan sojan kasa
Rundunar tsaro ta fito ta bayyana cewa wannan labari ƙarya ne tsagwaro wanda aka shirya don ta da hankalin jama’a da ɓata sunan sojojin ƙasar nan.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
