Fasahar AI Za Ta Kawo Matsala a Ayyukan Mutane? Sheikh Isa Pantami Ya Yi Bayani
- Farfesa Isa Ali Pantami ya kwantar da hankulan masu fargabar cewa mutane za su iya ra ayyuka saboda zuwa fasahar AI
- Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani ya ce fasahar AI za ta samar da damarmakin ayyuka ga wadanda suka samu kwarewa
- Pantami ya jaddada cewa fasahar zamani na taka muhimmiyar rawa wajen inganta harkokin ilimi da bunkasa tattalin arziki
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bauchi, Najeriya – Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya bayyana cewa fasahar zamani kamar AI ba za ta kwace ayyukan mutane ba.
Pantami, wanda babban malamin addinin Musulunci ne ya ce maimakon haka fasaha za ta samar da sababbin damarmakin aiki ga waɗanda suka kware a harkar.

Source: Facebook
Ya bayyana haka ne yayin da yake jawabin bude babban taron farko na ƙasa kan ilimi, wanda sashen Ilimin Fasaha na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) ya shirya, in ji Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taron wanda ya gudana a dakin taro na CBN da ke harabar jami’ar ATBU, Bauchi ya samu halartar manyan masana da masu bincike daga sassa daban-daban na Najeriya da ƙetare.
Fasahar AI za ta kwace ayyukan mutane?
Tsohon ministan ya jaddada cewa AI na taka muhimmiyar rawa a ci gaban ilimi da tattalin arziki, yana mai cewa babu wata ƙasa da za ta cigaba idan ta yi watsi da wannan sabuwar fasaha mai canza duniya.
Ya ce duk da cewa ilimin na da muhimmanci, amma shigar da AI a cikin tsarin koyarwa da koyo ya zama wajibi domin ƙara inganci da haɓaka tattalin arziki.
“Tsoron da ake cewa fasahar AI za ta kwace ayyukan mutane ba gaskiya ba ne. AI ba za ta iya karbe aikin kowa ba.
"Amma waɗanda suka kware wajen amfani da AI su ne za su samu ayyuka a nan gaba. Don haka, kowa ya nemi ilimi kan yadda ake amfani da ita.”
Pantami ya ba shugabanni shawara
Farfesa Pantami ya kuma shawarci gwamnoni, ’yan majalisa da hukumomin ilimi su saka karatun AI cikin jadawalin makarantu daga matakin firamare zuwa jami’a.
Tsohon Ministan ya nanata cewa makomar kowace ƙasa a yanzu na iya dogara ne da ilimin fasaha da kirkire-kirkire.

Source: Facebook
A nasa jawabin, Shugaban Jami’ar ATBU, Farfesa Ibrahim Hassan Garba, ya bayyana taron a matsayin sabuwar kafa da za ta canza tsarin Ilimin Fasaha a jami’ar.
Ya ce:
“Duniya na canzawa cikin sauri zuwa tsarin fasahar zamani da bin tsari mai daidaito. Ya zama wajibi mu kasance cikin shiri domin kada mu makara wajen wannan sauyi.”
Pantami ya yi maganar fitowa takara a 2027
A wani rahoton, kun ji cewa Farfesa Isa Ali Pantami ya bayyana cewa zai sanar da matsayarsa kan fitowa takarar gwamnan jihar Gombe idan lokaci ya yi.
Pantami, tsohon ministan sadarwa a Najeriya ya tabbatar da cewa jama'a na ta kiraye-kiraye da rokon ya nemi kujerar gwamnan Gombe a 2027.
Ya bayyana cewa zuwa yanzu ya gama tuntuɓar waɗanda ya kamata kan lamarin da kusan 97% kuma ya sha alwashin bayyana matsayarsa idan lokaci ya yi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


