Dubu Ta Cika: NSCDC Ta Cafke Shahararrun Barayi da Suka Addabi Yankuna 3 a Kano
- Hukumar NSCDC ta kama mutane hudu da ake zargi da fasa gidaje suna sata a yankunan Dambatta, Fagge da Tarauni
- NSCDC ta ce an gano wayoyi, talabijin, tayoyi, da na’urori masu amfani da hasken rana a hannun wadanda ake zargi
- Kwamandan NSCDC na Kano, Bala Bodinga ya ce za a gurfanar da su a kotu, ya kuma nemi hadin kai daga al'ummar jihar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Hukumar tsaron farar hula (NSCDC) reshen jihar Kano ta tabbatar da kama wasu mutane hudu da ake zargi da aikata laifuffukan sata.
NSCDC ta ce an kama gaggan barayin ne bayan da aka samu rahoton aika-aikar fasa gidaje, satar kayayyaki, da lalata kadarori da suke yi a Kano.

Source: Facebook
An kama shahararrun barayi a Kano
Mai magana da yawun hukumar, Ibrahim Abdullahi, ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Juma’a, in ji rahoton Punch.
Ibrahim Abdullahi ya ce an kama matasan hudu ne a yayin aikin sintiri da tsaurara tsaro da hukumar ke gudanarwa don magance laifuffuka a jihar.
“A ƙoƙarinmu na tabbatar da tsaro a fadin Kano, mun kama wasu shahararrun masu fasa gidaje da satar kayayyaki a yankuna uku na jihar.
"Yankunan da suka dade suna addaba sun hada da Dambatta, Fagge da Tarauni, kuma duk sun amsa laifuffukansu bayan an kama su da kayayyakin da suka sata."
- Ibrahim Abdullahi.
An kwato kayayyaki a hannun barayin
Hukumar NSCDC ta bayyana cewa ta kwato kayayyaki masu yawa daga hannun wadanda ake zargin, ciki har da wayoyi tara, talabijin daya, fankoki uku, tayoyin mota uku, da kuma na’urori masu amfani da hasken rana hudu.
Sauran kayan satan da aka kwato sun hada da lasifika, ƙarfen taga, wayoyi biyu, keken hawa, da ƙaramin janareta.
“Kama waɗannan mutane wani ɓangare ne na yunƙurinmu na dakile ayyukan ‘yan fashi da masu lalata kadarorin gwamnati da na jama’a a Kano,” in ji NSCDC.
Sanarwar ta ce an gudanar da cikakken bincike kan lamarin kuma an gano cewa wadanda ake zargin sun shafe lokaci suna addabar al’umma, musamman a yankunan da ke da karancin jami’an tsaro.

Source: Original
Za a gurfanar da barayin a kotun Kano
Mai magana da yawun NSCDC ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu nan ba da jimawa ba, domin su girbi abin da suka dade suna shukawa.
Ya kuma tabbatar da cewa kwamandan NSCDC na jihar, Bala Bodinga, ya jajirce wajen ganin an kare kadarorin gwamnati da rayukan jama’a.
Abdullahi ya kuma roki jama’a su rinka ba da bayanai masu amfani ga jami’an tsaro idan suka ga abin da ke da alaka da laifi a unguwanninsu, inji rahoton Stallion Times.
NSCDC ta ki karbar cin hancin N10m
A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar NSCDC ta cafke wasu ‘yan bindiga guda biyu da suka addabi kananan hukumomi biyar a Sokoto.
Kwamandan NSCDC a jihar Sokoto, Muhammad Dada, ya ce Alhaji Koire da Alhaji Buba ’yan fashi ne masu hadari dake da yan bindiga sama da 300 a sansaninsu.
Yayin da aka kama gaggan 'yan bindigar, sai suka 'yan ta’addan suka yi yunkurin ba jami'an NSCDC cin hancin N10m domin a bar su su gudu, amma ba a karba ba.
Asali: Legit.ng


