Abin da Wike Ya Ce bayan Yaɗa Cewa Tinubu Ya Hana Shi Magana kan Gwamnatinsa
- Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya yi martani kan jita-jitar da ake yadawa game da rashin lafiyarsa da sauran rade-radi
- Wike ya ce shi ba mai magana ne da yawun Shugaba Bola Tinubu ba, duk da yana bayyana ayyukansa a babban birnin Abuja
- Ministan ya bayyana hakan ne a tattaunawar manema labarai, ya ce aikinsa shi ne sanar da jama’a ci gaban birnin tarayya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya (Abuja), Nyesom Wike, ya warware wasu rade-radi da dama da ake yaɗawa kansa.
Wike wanda shi ne tsohon gwamnan Rivers ya bayyana cewa ba shi ne mai magana da yawun Shugaba Bola Ahmed Tinubu ko gwamnatin tarayya ba, aikinsa daban ne.

Source: Twitter
Wike ya magantu kan matsala da Bola Tinubu
Wike ya yi wannan bayani ne yayin wata tattaunawar manema labarai da Leadership ta bibiya inda ya karyata wasu rahotanni da ake danganta shi da su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan ya fadi haka ne domin warware jita-jita inda ya ce abin da yake yi duk wata a Abuja shi ne wayar da kan mutane game da ayyukan da yake yi.
Ya ce wannan magana ta biyo bayan yadda wasu ke ganin cewa yana magana da yawun shugaban ƙasa ne saboda yana bayyana ayyukan da ke gudana a Abuja.
Wike ya ce aikinsa shi ne sanar da duniya abin da ke faruwa a karkashin gwamnatin Tinubu da kuma irin ci gaban da ake samu a birnin tarayya.
Ya ce:
“Ba ni ne mai magana da yawun gwamnati ba. Na dai saba bayyana abin da ke gudana a Abuja, don mutane su sani."

Source: Twitter
Abin da Nyesom Wike ya sanya a gaba
Wike ya kara da cewa aikinsa na ministan Abuja ya haɗa da bayyana manufofi, tsare-tsare, da ayyukan ci gaban Abuja, ba wai magana da yawun gwamnatin tarayya ba.

Kara karanta wannan
"Ba zan yi sulhu da yan bindiga ba," Gwamna ya shirya daukar jami'an tsaro 10,000
Ya kuma yi watsi da rahotannin da ke cewa yana fama da rashin lafiya ko kuma shugaban ƙasa ya hana shi yin magana da ‘yan jarida, cewar Daily Post.
“Ina lafiya, ban taɓa yin rashin lafiya ba, kuma babu inda Shugaba Tinubu ya hana ni yin magana kan ci gaban Abuja."
- Nyesom Wike
Ministan ya ce yana mai da hankali ne kan ayyukan raya Abuja, yana kuma ganin wajibi ne a sanar da ‘yan Najeriya abin da ake yi.
Ya kammala da cewa ba zai damu da jita-jitar kafafen sada zumunta ba domin, a cewarsa ba su da wata ma’ana ga cigaban kasa.
Wike ya musanta shirin takara da Tinubu
Mun ba ku labarin cewa an yada wata jita-jita cewa ana shirin tursasa Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi takara da Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.
Sai dai, Ministan ya warware zare da abawa inda ya bayyana matsayarsa kan yin takarar shugaban kasa a shekarar 2027.
Nyesom Wike ya bayyana cewa har yanzu bai sauya ba daga kan goyon bayan da yake ga shugaban kasa Bola Tinubu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
