John Zuya: 'Yan Sanda Sun Cafke Wanda ake Zargi da Kashe Mawakin Gargajiya

John Zuya: 'Yan Sanda Sun Cafke Wanda ake Zargi da Kashe Mawakin Gargajiya

  • ‘Yan sanda a karamar hukumar Tafawa Balewa ta jihar Bauchi sun kama wani mutum da ake zargi da hannu a kisan mawaki, John Zuya
  • Zuya, wanda fitaccen mawaki ne a tsakanin al’ummar Sayawa, ya rasu bayan dawowarsa daga Lagos inda ya yi bajinta a gaban masoyansa
  • Rahotanni sun bayyana cewa wani abokinsa mai suna Emmanuel Wakili ne ake zargi da kashe shi saboda kishi, kuma bincike na ci gaba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Bauchi – Rundunar ‘yan sanda ta jihar Bauchi ta kama wani mutum da ake zargi da hannu a mutuwar mawaki, John Zuya, wanda rasuwarsa ta tayar da hankali a Tafawa Balewa.

Rahotanni sun nuna cewa Zuya ya rasu cikin yanayi mai cike da rudani bayan dawowarsa daga Lagos, inda ya gudanar da wani gagarumin taro.

Kara karanta wannan

Babu dadin ji: An tsinci gawar soja a wani irin yanayi bayan bin 'dan bindiga' cikin daji

John Zuya
John Zuya da ya mutu baya dawowa daga Legas. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattara bayanai kan halin da ake ciki game da kisan ne a wani sako da Zagazola Makama ya wallafa a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutuwarsa ta haifar da tashin hankali da jimami a tsakanin ‘yan uwansa da mazauna yankin, inda mutane da dama ke neman a tabbatar da adalci.

Zargin kisan Zuya da bidiyon da ya bayyana

Bayan rasuwar mawakin, wani mutum mai suna Yakubu Alhamdu, wanda shi ne mataimakin shugaban kungiyar Zayoda reshen Tafawa Balewa, ya fitar da wani bidiyo.

A bidiyon da aka ce ya wallafa a intanet, Alhamdu ya yi ikirarin cewa wani mawaki, Emmanuel Wakili, ne ya kashe Zuya.

A cewar Alhamdu, Wakili ya amsa cewa ya kashe abokinsa saboda kishi da hassada, yana mai cewa ya “kama kurwarsa” cikin wata karamar jaka sannan ya bugi kansa har ya mutu.

Alhamdu ya bayyana cewa hakan ne ma ya jawo jinin da aka gani a goshin Zuya bayan rasuwarsa, abin da ya kara tabbatar da shakku a zukatan mutane game da yadda lamarin ya faru.

Kara karanta wannan

Hukumar DSS ta yi babban kamu a jihar Kaduna, an bankado masu safarar makamai

‘Yan sanda sun kama wanda ake zargi

Bayan yada wannan bidiyo da kuma koke-koken jama’a, rundunar ‘yan sanda a Bauchi ta fara bincike mai zurfi domin gano gaskiyar lamari.

Bayan wani dan lokaci, jami’an tsaro suka samu nasarar gano inda wanda ake zargi, Emmanuel Wakili, yake, suka kuma cafke shi a yankin Tafawa Balewa.

Sufeton 'yan sanda
Sufeton 'yan sandan Najeriya, IG Kayode. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Bayan tabbatar da kama wanda ake zargi, 'yan sanda na cigaba da gudanar da bincike domin gano hakikanin abin da ya faru.

Rasuwar John Zuya ta girgiza al’ummar Sayawa da dama, musamman ma saboda irin farin jininsa da tasirinsa a fagen waka.

Sojoji sun kama dan ta'adda, Badoo

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojin Najeriya sun tabbatar da kama kasurgumin dan ta'add aka fi sani da Babawo Badoo.

Bayanan da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa an kama Badoo ne jihar Filato a wani farmaki da dakarun sojin Najeriya suka kai masa.

A wani samame da rundunar ta kai a sassan Najeriya, ta kashe 'yan bindiga biyu tare da kama wasu sama da 20.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng