An Yi Rashin Dattijo: Tsohon Sakataren Gwamnati Ya Rasu Yana da Shekaru 104
- An shiga jimami a jihar Kwara bayan sanar da rasuwar dattijo kuma sakataren gwamnati a jihar na farko
- Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya yi jimamin rasuwar marigayin, Sir Joseph Aderibigbe, wanda ya rasu yana da shekara 104
- Gwamnan ya ce marigayi Aderibigbe mutum ne mai kishin kasa da sadaukarwa wajen gina jihar Kwara tun daga farkon kafuwarta
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ilorin, Kwara - Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan tsohon sakataren gwamnati.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa an yi rashin dattijon, Sir Joseph Adeniyi Aderibigbe, wanda ya rasu yana da shekara 104.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa daga kakakinsa, Rafiu Ajakaye ya sanyawa hannu da aka wallafa a shafin Facebook na gwamnatin jihar a jiya Alhamis 23 ga watan Oktobar 2025 da muke ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Takaitaccen tarihin marigayin da hidimar da ya yi
Rahotanni sun tabbatar da cewa marigayin shi ne ya fara rike mukamin sakataren gwamnatin jihar wanda ya ba da gudunmawa sosai.
Tsohon ma'aikacin gwamnatin wanda asalinsa daga Erin-Ile a ƙaramar hukumar Oyun ta jihar, ya kasance Shugaban Ma’aikata a lokaci guda da yake Sakataren Gwamnatin Jihar.
Ya rike mukamin ne a lokacin da tsohon gwamnan jihar na soja, Birgediya David Bamigboye, ya kasance gwamnan farko na jihar daga 1967 zuwa 1975.

Source: Facebook
Gwamna ya yi jimamin rasuwar dattijo a Kwara
Bisa ga bayanin ɗansa, Barista Debo Aderibigbe, tsohon jami’in gwamnatin ya rasu cikin salama a Ilorin da safiyar jiya Laraba bayan rayuwa mai albarka.
Gwamnan ya bayyana Aderibigbe a matsayin ginshiƙi mai gaskiya, kishin ƙasa, wanda ya ba da gudunmawa a jihar.
Ya ce mutuwar marigayi Aderibigbe ta kawo ƙarshen wani lokaci na sadaukarwa ga aikin gwamnati da son cigaban jihar Kwara tun daga farko.
Gwamnan ya ƙara da cewa Aderibigbe zai ci gaba da zama abin tunawa saboda jajircewarsa da kyakkyawan shugabanci ga ma’aikatan gwamnati.
AbdulRazaq ya roƙi Allah ya ji ƙan marigayi, ya ba iyalansa, abokansa, da al’ummar Erin-Ile haƙuri da ƙarfin zuciya wajen jure rashin nasa.
Sanarwar ta ce:
"Wannan rasuwar Baba Aderibigbe ta kawo ƙarshen wani lokaci na shahara da kishin ƙasa, sadaukarwa ga hidimar jama’a, da ƙoƙarin gina Jihar Kwara ta zama abin koyi a cikin jihohin ƙasa.
"Za a tuna sohon sakataren gwamnatin jihar saboda kyakkyawan ayyukansa na hidimar jama’a da jagorancinsa tsawon shekaru.
"Ina addu’ar Allah ya jikansa da rahama, ya kuma ba iyalansa da al’ummar Erin-Ile gaba ɗaya haƙuri da ƙarfin guiwa."
Gwamna ya jajanta kan rasuwar malamin Musulunci
A wani labarin, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana bakin ciki bisa rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci na Ilorin a jihar.
AbdulRazaq ya jajanta wa iyalai, almajirai da mabiyan malamin, inda ya bayyana shi a matsayin mutum mai tasiri da gagarumar gudummawa.
Gwamnan ya yi addu’a Allah ya gafarta masa, ya ba shi Aljannah Firdausi, tare da ba iyalansa da mabiyansa juriya kan rashin da aka yi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

