Rusau Ya Taɓa Musulmai: Gwamna Ya Rushe Kasuwa, an Taba Masallaci a Lagos
- Al'ummar Musulmi sun koka bayan gwamnatin Legas ta taɓa masallaci yayin rushe-rushe cikin kasuwa wanda ya jawo asarar dukiya
- Gwamnatin Jihar Lagos ta rushe kasuwar Costain, inda ta kori ‘yan kasuwa da dama tare da lalata kadarori na miliyoyin Naira
- Shaidu sun ce jami’an hukumar LASTMA da KAI sun isa wurin da rana, suka tarwatsa jama’a da hayaki mai sa hawaye kafin rushe masallaci
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - Dubban ‘yan kasuwa sun rasa wuraren kasuwancinsu, kuma an lalata kadarori masu darajar miliyoyin Naira.
Lamarin ya faru ne yayin rushe kasuwar Costain da gwamnatin jihar Lagos ta yi ranar Alhamis 23 ga watan Oktobar 2025 da muke ciki.

Source: Getty Images
Gwamnan Lagoa ya rusa masallaci da kasuwa
Rahoton Tribune ya ce jami'an hukumomin LASTMA da KAI suka gudanar da aikin rusau din domin tsaftace muhalli a yankin.

Kara karanta wannan
Babu dadin ji: An tsinci gawar soja a wani irin yanayi bayan bin 'dan bindiga' cikin daji
Hakan ya faru ne karkashin jagorancin mai ba gwamna shawara kan sufuri, Mista Sola Giwa.
Shaidu sun bayyana cewa jami’an sun zo da manyan injinan tono da ‘yan sanda, suka watsa jama’a da hayaki mai sa hawaye kafin rushe shaguna da masallaci.
Wasu ‘yan kasuwa sun koka cewa babu gargadi kafin rushewar, Alfred Wisdom, mai yin kayan ciye-ciye, ya ce ya yi asarar sama da Naira miliyan biyar.
Ya bayyana bakin cikinsa yana cewa hakan ya faru watanni shida bayan rushe Otumara da ta tilasta dubban mutane barin gidajensu.

Source: Original
Liman ya yi korafi kan rusa masallaci a Lagos
Wuraren addini ma ba su tsira ba, limamin masallacin Markaz-ul-Mahani, Ustaz Abdulsallam Olawale, ya tabbatar da cewa an rushe masallacin da gine-gine kusa da shi.
Ya ce jami’an sun fara da bus-bus, daga bisani suka kai farmaki ga ‘yan kasuwa da masu ibada, inda kayan da aka adana suka salwanta gaba ɗaya.
Limamin ya roƙi Gwamna Sanwo-Olu da ya kula da wahalar mutane da rushewar ta jawo, tare da nuna tausayi ga wadanda abin ya shafa.
Sarki ya yi Allah wadai da rusau
Sarkin Otumara, Cif Kehinde Kalejaiye, ya bayyana rusau din a matsayin sabawa doka, yana cewa filin yana da takardun gwamnati na tarayya.
Ya zargi jami’an gwamnati da amfani da karfin iko wajen zaluntar ‘yan kasuwa marasa laifi, yana roƙon gwamnati ta kawo ƙarshen irin wannan aiki.
Har zuwa lokacin da aka wallafa labarin, gwamnatin Lagos ba ta fitar da sanarwa ko alkawarin diyya ga ‘yan kasuwar da abin ya shafa ba.
Ana zargin gwamnan Lagos ya rusa masallatai 40
A baya, kun ji cewa gamnatin jihar Lagos ta rusa fiye da masallatai 40 da shaguna 3,000 na 'yan Arewa da ke kasuwanci a kasuwar Alaba Rago.
Wazirin Sarkin kasuwar Alaba Rago, Alhaji Adamu Katagum ya ce gwamnati ta rusa kasuwar da suka shafe shekaru 45 suna ginawa.
Wani dan kasuwa, Alhaji Muhammed Rabiu ya ba da labarin yadda jami'an tsaro suka rusa kasuwar, suka raba su da dukiyarsu.
Asali: Legit.ng

