Zaben 2027: ICAN Ta Yi Hangen Nesa, Ta Gano Babbar Barazana ga Darajar Naira

Zaben 2027: ICAN Ta Yi Hangen Nesa, Ta Gano Babbar Barazana ga Darajar Naira

  • Shugaban kungiyar kwararrun akantoci ta ICAN, Chidi Ajaegbu, ya ce Naira na iya fuskantar babbar matsala a nan gaba
  • Ya bayyana cewa bayan babban zaben 2027, darajar Naira za ta iya faduwa warwas saboda wasu dalilai
  • Chidi Ajaegbu ya kuma gargadi gwamnati kan yawan karbo bashi da ke jawo matsin tattalin arziki a Najeriya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Shugaban ƙungiyar masu akantoci ta kasa (ICAN), Chidi Ajaegbu, ya yi gargadin cewa darajar Naira na iya sake ruguzowa.

Ya ce darajar kudin kasar nan zai fadi bayan zaɓen 2027, idan gwamnati ta ci gaba da karbo bashi ba tare da tsarin inganta kasa na.

ICAN ma fargaba kan darajar Naira
Hoton gwamnan CBN, Olayemi Cardoso da Naira Hoto: Central Bank of Nigeria
Source: UGC

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Ajaegbu, ya fadi haka ne a yayin wata lacca da jami’ar Godfrey Okoye ta shirya .

Kara karanta wannan

Injiniyoyi sun ga kokarin Gwamna Abba, sun ba shi lambar girmamawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi wa taron taken “Amfani da kasuwar hannayen jari wajen gina ababen more rayuwa da sauya tattalin arzikin Najeriya.”

ICAN ta gargadi gwamnatin Najeriya

Jaridar Guardian ta wallafa cewa Ajaegbu ya ce gwamnatin Najeriya na karban bashin da zai iya jefa tattalin arzikin ƙasa cikin mawuyacin hali.

A kalamansa:

"Yawan ɗaukar bashi na tsoratar da masu saka jari. Gwamnati ta zama mai taka-tsantsan, domin tsohon shugaba Muhammadu Buhari ya yi sakaci da lamunin da ya karba."

Ajaegbu, wanda shi ne shugaban kamfanin Heritage Capital Market Ltd, ya ƙara da cewa:

“Kwana kaɗan bayan zaɓen 2027, ana iya rage darajar Naira. Duk da cewa Naira ta daidaita cikin watanni shida da suka gabata, hakan na iya sauyawa bayan zaɓen.”

Masana sun fadi amfanin kasuwar hannayen jari

Shugaban majalisar dokokin Enugu, Uche Ugwu, ya jaddada muhimmancin kasuwar hannayen jari wajen haɓaka kasuwanci da inganta ci gaban ababen more rayuwa.

Kara karanta wannan

Najeriya ta sake martani kan harajin Trump da bukatar karbar baki daga Amurka

Haka kuma, Farfesa Uche Uwaleke, shugaban ƙungiyar Capital Market Academics of Nigeria (CMAN), ya ce ya zama dole a wayar da kan ‘yan ƙasa game da kasuwar hannayen jari.

Ya ce:

“Matakin sanin kasuwar hannayen jari a Najeriya yana da rauni sosai, musamman a yankin Kudu maso Gabas. Amma wannan tattaunawa za ta taimaka wajen ƙara fahimtar muhimmancin kasuwar hannayen jari a yankin."

Shugabar kwamitin shirya taron, Farfesa Uche Lucy Onyekwelu, ta ce kasuwar hannayen jari tana da rawar gani wajen jawo masu zuba jari.

Ta kuma nuna damuwa kan yadda yawancin kamfanoni a yankin Kudu maso Gabas ba su shiga kasuwar hannayen jari ba, inda ta ce hakan yana dakile ci gabansu.

Farfesa John Odo daga sashen lissafi da kuɗi na jami’ar Godfrey Okoye ya ce kasuwar hannayen jari tana taka muhimmiyar rawa wajen ɗaga tattalin arziki ta hanyar ba da dama ga kasuwanni da samar da ayyukan yi.

"Mun ceto Naira": Inji Shugaba Tinubu

A baya, kun ji cewa 2025, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ikirari cewa gwamnatin sa ta dawo da darajar Naira bayan matsalar da ta shiga a baya.

Kara karanta wannan

NNPP ta fadi hadarin dawo da zaben 2027 zuwa 2026 a Najeriya

Tinubu ya ce waɗannan sauye-sauye sun kawo daidaito tsakanin kasuwar musayar gwamnati da ta bayan fage, wanda a baya ya dakile hanyar almundahana.

Ya ƙara da cewa farashin canji tsakanin Naira da Dalar Amurka yanzu ba ya dogara da farashin danyen mai a kasuwar duniya kamar yadda ya ke a baya kafin manufofinsa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng