Majalisar Wakilai na Son Rage Ikon Shugaban Kasa kan Hukumar EFCC

Majalisar Wakilai na Son Rage Ikon Shugaban Kasa kan Hukumar EFCC

  • Majalisar Wakilai ta yi karatu na biyu ga kudirin dokar da ke neman gyara dokar kafa EFCC domin ba ta cikakken ‘yanci
  • 'Dan majalisa daga jihar Filato, Hon. Yusuf Gagdi, ne ya gabatar kudirin domin kare hukumar daga tasirin 'yan siyasa
  • Kudirin na neman hana shugaban kasa ikon cire shugaban EFCC sai da amincewar kashi 3 bisa 3 na 'yan majalisar dokoki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Majalisar wakilai ta amince da kudirin doka karo na biyu da ke neman gyara dokar kafa EFCC domin tabbatar da cikakken ‘yancin hukumar.

An gabatar da kudirin ne a zauren majalisa, yayin da dan majalisa daga jihar Filato, Yusuf Gagdi, ya jagoranci tattaunawa kan muhimman dalilan kudirin.

Yan majalisar wakilai a Abuja
Shugaba Bola Tinubu a majalisar wakilai. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Punch ta rahoto Gagdi ya ce gyaran dokar zai ba EFCC karfi wajen bin hanyoyin da masu laifi ke bi a wannan zamani, tare da tabbatar da daidaito da ka’idojin yaki da cin hanci na kasa da kasa.

Kara karanta wannan

Daliban jami'a za su yi karatu kyauta saboda tallafin gwamna Umaru Bago

Manufofin gyaran dokar EFCC a Najeriya

Yusuf Gagdi ya ce tun bayan kafa hukumar a 2004, harkokin laifuffukan kudi sun fadada, sun hada da laifuffukan intanet, amfani da kudin Kirifto, da safarar kudi ta haram.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa dokar ta tsufa, kuma ba ta bayar da cikakken kariya ga hukumar daga tasirin siyasa, wanda hakan ke rage amincewar jama’a da ita.

A cewarsa:

“EFCC na aiki ne bisa tanade-tanaden doka da zamaninsu ya wuce, wadanda ba su dace da yanayin laifuffukan kudi na yanzu ba, kuma hakan yana sanya hukumar cikin tasirin siyasa.”

Rage ikon shugaban kasa kan EFCC

Daya daga cikin muhimman abubuwan da kudirin ya kunsa shi ne rage ikon shugaban kasa wajen cire shugaban EFCC.

Yusuf Adamu Gagdi
Yusuf Gagdi yayin gabatar da kudirin EFCC a majalisa. Hoto: Hon. Yusuf Adamu Gagdi
Source: Facebook

A dokar da ake amfani da ita yanzu, shugaban kasa na da ikon cire shugaban hukumar ba tare da amincewar majalisa ba.

Sai dai sabon kudirin ya tanadi cewa dole sai majalisar dattawa da ta wakilai sun amince da kashi biyu bisa uku (2/3) kafin shugaban kasa ya iya cire shugaban EFCC daga mukaminsa.

Kara karanta wannan

Babu dadin ji: An tsinci gawar soja a wani irin yanayi bayan bin 'dan bindiga' cikin daji

Hon. Gagdi ya ce wannan gyara zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiyar hukumar da kuma tabbatar da cewa tana aiki ba tare da tsoron tsoma bakin 'yan siyasa ba.

Amfanin kudirin ga yaki da rashawa

Dan majalisar ya bayyana cewa wannan kudiri zai karfafa tsarin yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, tare da mayar da hukumar EFCC mai zaman kanta da ta dace da tsarin kasa da kasa.

Ya ce:

“Wannan gyara zai taimaka wajen tabbatar da cewa EFCC ta zama cibiyar da ke aiki cikin gaskiya, ‘yanci, da kwarewa, wadda ke da karfin magance laifuffukan kudi na zamani.”

Daily Trust ta rahoto cewa ya kara da cewa hakan zai kara martabar Najeriya a idon duniya, tare da kawo ci gaba a tsarin tattalin arziki da amincewar jama’a ga yaki da cin hanci.

EFCC: Okowa bai tsira ba har yanzu

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar EFCC ta ce har yanzu tana bincike kan tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa.

Hakan na zuwa ne bayan tsohon gwamnan ya koma jam'iyyar APC mai mulki daga PDP tare da gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

Abin da Tinubu ya gayawa sabon shugaban INEC bayan rantsar da shi

Ifeanyi Okowa dai ya kasance jigo a PDP kafin sauya shekar, inda ya yi takarar mataimakin shugaban kasa tare da Atiku Abubakar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng