Babu Dadin Ji: An Tsinci Gawar Soja a Wani Irin Yanayi bayan Bin 'Dan Bindiga' cikin Daji

Babu Dadin Ji: An Tsinci Gawar Soja a Wani Irin Yanayi bayan Bin 'Dan Bindiga' cikin Daji

  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa sojan kasan Najeriya ya rasa ransa bayan bin wani da ya kai musu hari da sanda a jihar Kwara
  • Rahotanni sun ce sojan mai suna Usman Alhaji ya bi maharin cikin daji amma bai dawo ba, sai dai aka tsinci gawarsa washegari
  • ’Yan sanda sun gano raunukan wuka a wuyan mamacin, sannan aka mika gawarsa ga iyalai domin birne shi bisa tsarin Musulunci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ilorin, Kwara - Al'ummar wani yanki a jihar Kwara sun shiga fargaba bayan samun gawar wani soja a cikin daji.

An gano gawar sojan a kauyen Twatagi, karamar hukumar Patigi ta Jihar Kwara, bayan ya bi wani da ya kai musu hari cikin daji.

An fara bincike bayan samun gawar soja a daji
Dakarun sojoji yayin ran gadi a cikin daji. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Rahoton Zagazola Makama ya bayyana cewa lamarin ya faru ne ranar 21 ga Oktobar 2025, da misalin ƙarfe 5:30 na yamma a hanyar Patigi.

Kara karanta wannan

Gwamna ya kakaba haraji kan masu jana'za, aure da suna? An ji gaskiyar lamari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kokarin sojoji na dakile rashin tsaro a Kwara

Jihar Kwara dai na daga cikin jihohin Arewa ta Tsakiya da ke fama da matsalar yan bindiga wanda ke kara ta'azzara a kullum.

Dakarun sojoji na iya bakin kokarinsu domin ganin sun kawo karshen yan bindiga da kuma masu daukar nauyinsu.

Ko a kwanan nan, rundunar sojin Najeriya ta ceto mutane 21 da aka sace a kwanan nan, ciki har da wasu ‘yan kasar China guda hudu.

An kaddamar da farmakin ne a karkashin Operation FANSAN YAMA domin murkushe ‘yan bindiga a Arewa ta Tsakiya.

Kwara: An tsinci gawar soja a daji

Marigayin mai suna Usman Alhaji, wanda ke aiki a Apapa, Lagos, yana tafiya ne a babur tare da wani matashi mai suna Muhammad Baba.

A cewar majiyoyi, yayin da suke tafiya, suka hadu da wani mutum da ke tafiya da sanda wanda sai kawai ya kai musu duka yayin da suka wuce.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kashe hatsabibin dan bindiga Abu AK da ya shiga gari cin kasuwa

Mutumin ya tsere cikin daji, sai sojan ya sauka daga babur ya bi shi, amma bai dawo ba har zuwa dare.

Bayan jiran lokaci mai tsawo babu labarinsa, Muhammad Baba ya shiga neman sa cikin daji amma bai same shi ba.

Yan sanda sun kaddamar da bincike samun gawar soja a Kwara
Taswirar jihar Kwara da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Yan sanda suna bincike kan lamarin

Washegari da misalin ƙarfe 2:00 na rana, mazauna yankin suka gano gawar sojan cikin daji.

’Yan sanda da jami’an tsaro sun isa wurin domin bincike, inda suka gano cewa sojan ya samu raunin wuka a wuya.

An mika gawar marigayin ga iyalansa domin binne shi bisa tsarin Musulunci, yayin da bincike ke ci gaba don gano wanda ya aikata laifin.

An musanta cewa yan bindiga sun mamaye Kwara

Mun ba ku labarin cewa gwamnatin Kwara ta yi karin haske kan wasu maganganun da ke cewa 'yan bindiga sun mamaye wasu kananan hukumomi a jihar.

Ta zargi 'yan adawa a ciki da wajen jihar kan yada labarai na karya dangane da batun matsalar rashin tsaro da ke damun jihar Kwara baki daya.

Gwamnatin ta kuma nuna yatsa ga Peter Obi kan yada abubuwan da ba haka suke ba dangane da rashin tsaron jihar a shafukan sada zumunta.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.