Abin da Tinubu Ya Gayawa Sabon Shugaban INEC bayan Rantsar da Shi

Abin da Tinubu Ya Gayawa Sabon Shugaban INEC bayan Rantsar da Shi

  • Sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Ojo Amupitan ya kama rantsuwar aiki
  • Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da sabon shugaban na hukumar INEC a fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja
  • Mai girma Tinubu ya tunatar da Farfesa Amupitan nauyin da ya hau kansa tare da abin da yake so ya aiwatar a hukumar INEC

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) a matsayin shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).

Shugaba Tinubu ya rantsar da Farfesa Amupitan ne a wani gajeren biki da aka gudanar a zauren majalisar zartarwa da ke fadar shugaban kasa, Abuja, a ranar Alhamis.

Tinubu ya yi kira ga shugaban INEC
Sabon shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan da Shugaba Bola Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Me Tinubu ya gayawa Amupitan?

Jaridar Daily Trust ta ce bayan rantsarwar, Shugaba Tinubu ya bukaci sabon shugaban na INEC da ya gudanar da aikinsa cikin gaskiya, amana da biyayya ga doka, tare da kiyaye martabar hukumar.

Kara karanta wannan

Magana ta kare, Tinubu ya rantsar da sabon shugaban hukumar zaben Najeriya

“Nadinka da kuma amincewar majalisar dattawa da ta biyo bayan haka, alama ce ta cancantar ka da amincewar da majalisun zartarwa da na dokoki suka nuna a gare ka."
“Wannan babban matsayi da ka samu wani sabon tafarki ne mai kalubale, amma kuma mai cike da lada. Ina da yakinin za ka gudanar da aikinka da cikakken kishin kasa, da himma, da nagarta.”

- Shugaba Bola Tinubu

Tinubu ya yaba da dimokuradiyyar Najeriya

Shugaba Tinubu ya jaddada cewa tun daga shekarar 1999, Najeriya ta samu ci gaba wajen karfafa tsarin dimokuradiyya da hukumomin gudanar da zabe, inda ya ce dole ne a ci gaba da inganta tsarin domin tabbatar da sahihancin zabubbuka.

“Dimokuradiyyarmu ta yi nisa sosai a cikin shekaru 25 da suka gabata. Mun karfafa hukumominmu, musamman hukumar zabe ta kasa, ta hanyar sababbin dabaru da gyare-gyare.”

- Shugaba Bola Tinubu

Ya bayyana cewa zaben gwamnan jihar Anambra da za a gudanar a ranar 8 ga Nuwamba, 2025, zai zama gwajin farko ga sabon shugaban na INEC, za a samu labarin a rahoton The Guardian.

Kara karanta wannan

Shugaban INEC mai jiran gado ya isa fadar shugaban kasa da ke Abuja, an samu bayanai

"Yana da muhimmanci zabubbukanmu su kasance masu ’yanci, gaskiya, da amincewa. Dole ne mu ci gaba da gyara kura-kuran da suka gabata tare da kirkiro hanyoyin da suka dace da zamani.”
“Don kare amincewar jama’a ga zabubbuka, dole ne a kiyaye gaskiya da sahihancin tsarin. Daga rajista, yakin neman zabe, kafafen yada labarai, zabe da kirga kuri’u, duk ya zama cike da gaskiya, tsabta da natsuwa.”

- Shugaba Bola Tinubu

An rantsar da sabon shugaban hukumar INEC
Sabon shugaban hukumar INEC, Joash Ojo Amupitan Hoto: @NGRSenate
Source: Twitter

A karshe, Shugaba Tinubu ya umurci sabon shugaban INEC da ya tabbatar da cewa hukumar ta zama abin koyi wajen gudanar da zabe mai inganci da gaskiya a Najeriya.

“Ina umurtarka, Farfesa Amupitan, da ka kare martabar tsarin zabe, ka kuma karfafa karfin hukumar INEC domin ci gaban dimokuradiyyar Najeriya."

- Shugaba Bola Tinubu

Shugaban INEC ya magantu kan zabe

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Ojo Amupitan, ya yi tsokaci kan gudanar da sahihin zaben.

Farfesa Amupitan ya bayyana cewa zai tabbatar an gudanar da sahihin zabe a karakshin jagorancinsa.

Shugaban na INEC ya bada tabbacin cewa za a gudanar da zabe mai cike da gaskiya da adalci wanda kowa zai yi na'am da shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng