EFCC Ta Fadi Abin da Za Ta Yi kan Tuhumar Tsohon Gwamna da Ya Koma APC

EFCC Ta Fadi Abin da Za Ta Yi kan Tuhumar Tsohon Gwamna da Ya Koma APC

  • Hukumar EFCC ta bayyana makomar tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa kan tuhumarsa da ake yi
  • EFCC ta ce tuhumar da ake yi wa Okoowa na nan duk da komawarsa jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya
  • Daraktan Shari’a na EFCC, Sylvanus Tahir, ya ce babu wani ɗan siyasa da ya tsira daga bincike saboda shiga jam’iyyar da ke mulki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Hukumar EFCC ta yi karin haske kan tuhumar da ake yi kan tsohon gwamnan jihar Delta a Najeriya, Ifeanyi Okowa.

Hukumar ta bayyana cewa har yanzu Okowa yana ƙarƙashin bincike kan zargin almundahana, duk da komawarsa jam’iyyar APC.

EFCC Okowa
Tsohon gwamnan Delta da ya koma APC da Ofishin EFCC a Najeriya. Hoto: Ifeanyi Okowa, Economic and Financial Crimes Commission.
Source: Twitter

Komawa APC: EFCC ta musanta ba wasu kariya

Wannan bayani ya fito ne yayin taron manema labarai a Abuja da aka shirya domin cika shekaru biyu da Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, yake kan mulki, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Jiga jigan PDP 15 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a Zamfara, sun fadi dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daraktan Shari’a da Gurfanarwa na hukumar EFCC, Sylvanus Tahir, ya musanta jita-jitar cewa ’yan siyasa na samun kariya idan suka koma jam’iyyar da ke mulki.

“Wasu sun tambayi ko ’yan siyasa da suka koma jam’iyyar mai mulki ana kare su. Amsar gaskiya ita ce, ba haka ba ne.
“A fahimtata, shari’ar da ta shafi tsohon Gwamnan Jihar Delta har yanzu ana bincike, kuma adalci zai yi aiki a lokacin da ya dace.”

- Sylvanus Tahir

Duk da komawar Okowa APC, EFCC na ci gaba da bincikensa
Tsohon gwamnan jihar Delta a Najeriya. Hoto: Dr. Ifeanyi Arthur Okowa.
Source: Twitter

Matsayar EFCC kan bincken Okowa, yan siyasa

Rahoton TheCable ta ce Tahir ya bayyana cewa hukumar tana son tabbatar da cikakken bincike kafin kaiwa kotu, musamman idan shari’ar na da tasirin siyasa ko sunan babba.

Ya kara da cewa:

“Mun taba ganin yadda gaggawar kai shari’a kotu ta haifar da rashin sakamako mai kyau. Yanzu muna son yin aiki mai zurfi.
“Idan muka kai shari’ar kotu, ’yan Najeriya za su ga gaskiya. Ba mu da niyyar kare kowa saboda jam’iyyarsa.”

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Mutanen NNPP 500 sun bar bayan Kwankwaso, sun koma APC

Tahir ya ce duk da wasu na zargin EFCC da jinkiri wajen hukunta ’yan siyasa, hukumar tana kallon laifi a matsayin abu daya, ba laifi na musamman ba.

Ya bayyana cewa shari’o’in tsofaffin gwamnoni masu shekara takwas a mulki na bukatar cikakken bincike saboda yawan takardu da bayanai da ke tattare da su.

Jawabin Tahir ya zo ne a daidai lokacin da ake samun damuwa daga jama’a kan yadda wasu ’yan siyasa ke komawa jam’iyyar APC domin tsira daga hukunci.

EFCC ta tabbatar cewa ba za ta lamunci amfani da jam’iyya a matsayin mafaka ba, domin shari’a tana da kundinta.

Yadda EFCC ta kwato N500bn a mulkin Tinubu

Mun ba ku labarin cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta samu nasarori masu tarin yawa a yakin da take yi a Najeriya.

Kashim Shettima ya bayyana cewa hukumar ta samu nasarar kwato biliyoyin kudi cikin shekara biyu na mulkin Shugaba Bola Tinubu.

Mataimakin shugaban kasan ya nuna cewa hukumar ta kuma samu nasarar gurfanar da dubunnan mutane a gaban kotu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.