Kudirin da Aka Nemi Kirkiro Jiha 1 Ya Shiga Karatu na 2 a Majalisar Wakilan Najeriya
- Kudirin kirkiro karin jiha a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya ya tsallaka zuwa karatu na biyu a Majalisar Wakilai ranar Alhamis
- Hon. Olufemi Ogunbanwo da wasu yan Majalisar Tarayya uku ne suka dauki nauyin gabatar da kudirin wanda ya nemi a kafa jihar Ijebu daga Ogun
- Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu, wanda ya jagoranci zaman ya mika kudirin ga kwamitin gyaran kundin tsarin mulki
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Najeriya – Majalisar wakilai ta tarayya ta amince za ta yi wa kudirin kafa sabuwar jiha mai suna Ijebu daga cikin Jihar Ogun karatu na biyu.
Kudirin, wanda Hon. Olufemi Ogunbanwo, dan majalisa mai wakiltar Ijebu Ode/Ijebu North East/Odogbolu, da wasu ‘yan majalisa uku suka dauki nauyinsa, ya tsallaka zuwa karatu na biyu a zauren Majalisar Wakilai ranar Alhamis.

Source: Twitter
The Cable ta ruwaito cewa bayan kammala muhawara, mataimakin kakakin majalisar, Benjamin Kalu, wanda ya jagoranci zaman, ya mika kudirin ga kwamitin gyaran kundin tsarin mulki domin ci gaba da nazari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kalubalen kafa sabuwar jiha a doka
Majalisar dokoki ta ƙasa na ci gaba da aikin gyaran kundin tsarin mulkin 1999, wanda Benjamin Kalu ke jagoranta a matsayin shugaban kwamitin.
A cewarsa, aikin gyaran kundin tsarin mulkin zai kammala a watan Disamba na wannan shekarar 2025.
Sai dai kafa sabuwar jiha ko sake fasalin iyaka ba aiki ne mai sauƙi ba, domin doka ta shimfida matakai masu tsauri da goyon bayan jama’a, in ji Vanguard.
Ka'idojin da aka gindaya kan kirkiro jiha
A bisa tanadin sashe na 8(1) na kundin tsarin mulki, domin kafa sabuwar jiha, ana bukatar:
Kashi biyu bisa uku (2/3) na wakilan yankin da ke neman jihar su amince da kudirin a Majalisar Wakilai da Majalisar Dattawa, da kuma majalisar dokokin jiha da kananan hukumomin da abin ya shafa.

Kara karanta wannan
Sarkin Musulmi ya nuna yatsa ga kasashen Yamma kan zargin kisan Kiristoci a Najeriya
Bayan haka, sai a gudanar da zaben raba gardama a yankin da ake so a kafa sabuwar jiha, inda ake bukatar aƙalla kashi biyu bisa uku na mazauna yankin su zabi amincewa.
Ana bukatar sakamakon zaben raba gardama ya samu amincewar mafi rinjaye daga yan majalisun dokoki na jihohi a fadin ƙasa, kafin a kai ga amincewa ta kashi biyu bisa uku daga majalisar dattawa da wakilai domin ya zama doka.
Har yanzu, ba a ƙirƙiri sabuwar jiha ko a sake fasalin iyakokokin wasu jihohi ba tun bayan dawowar Najeriya kan tsarin mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999.

Source: Facebook
Majalisa ta yi magana kan canza lokacin zabe
A wani labarin, kun ji cewa Majalisar Wakilan Tarayya ta yi karin haske kan batun dawo zabe watan Nuwamban 2026 maimakon watan Fabrairu, 2027.
Shugaban kwamitin majalisar wakilai kan harkokin zabe, Adebayo Balogun, ya ce daga cikin dalilan akwai samar da isasshen lokaci don kammala karar zabe a kotu kafin a rantsar da sabon shugaban kasa.
Balogun ya ce ba a kai ga yanke matsaya a majalisar ba, domin a yanzu ra’ayoyi ne kawai ake tattarawa kafin a gabatar da rahoto da karatu na uku a majalisa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
