Fashewar Tankar Mai: Abubuwa 2 da Suka Jawo Fiye da Mutane 40 Suka Mutu a Neja

Fashewar Tankar Mai: Abubuwa 2 da Suka Jawo Fiye da Mutane 40 Suka Mutu a Neja

  • Hukumar NOA, ta bayyana cewa sakaci da lalacewar tarbiya ne suka haddasa gobarar tankar mai da ta hallaka mutane 42
  • NOA ta kuma gargadi mutane da cewa dibar man fetur daga tankar da ta fadi laifi ne, wanda ka iya kai mutum ga kurkuku
  • Wannan na zuwa ne, yayin da hukumar NEMA ta tabbatar da mutuwar mutum 42, ciki har da mata 24, maza tara da yara tara

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaban hukumar wayar da kai ta kasa (NOA), Lanre Issa-Onilu, ya ce sakaci da lalacewar dabi’u ne suka janyo fashewar tankar mai a Neja.

Lanre Issa-Onilu ya jaddada cewa, da ba don sakaci ba, to da kila yanzu mutane 42 da suka mutu a ƙauyen Essa, karamar hukumar Katcha na nan da ransu.

Kara karanta wannan

Abin da Tinubu ya gayawa sabon shugaban INEC bayan rantsar da shi

Hukumar NOA ta ce sakaci da rashin tarbiya ne suka jawo mutane 42 suka mutu a fashewar tankar mai a Neja
Jami'an hukumar kashe gobara ta tarayya, na kokarin kashe wuta a jikin tankar mai da ta fadi. Hoto: @Fedfireng
Source: Twitter

'Sakaci ya jawo fashewar tankar fetur' - NOA

A tattaunawarsa da tashar Channels TV ranar Alhamis, Issa-Onilu ya bayyana cewa abin da ya faru a Essa, abin takaici ne kwarai da gaske, wanda za a iya kauce masa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce bayan gobarar tankar mai da ta faru a kauyen Dikko a farkon shekarar nan, Shugaba Bola Tinubu ya ba NOA umarnin gudanar da wayar da kai a faɗin ƙasar.

Shugaban NOA ya ce duk da wayar da kai da ake yi, mutane na ci gaba da yin watsi da gargadin hukumar. Ya dora alhakin hakan kan rashin jagoranci mai nagarta a ƙauyuka.

“Mutane suna sane da irin haɗarin da ke tattare da dibar mai a motar da ta fadi, amma sakaci da lalacewar tarbiya ya sanya sun yi kunnen kashi. Wannan al’amari ya shafi kowa da kowa."

- Lanre Issa-Onilu.

‘Dibar mai laifi ne’ — Issa-Onilu

Kara karanta wannan

Bayan artabu mai zafi, sojoji sun dakile harin Boko Haram da ISWAP a jihohi 2

Issa-Onilu ya yi Allah-wadai da yadda jama'a ke dibar mai daga tankar da ta fadi, yana mai cewa hakan laifi ne kuma rashin tunani ne.

“Wannan fetur din da ya ke zuba, dukiyar wani ce, dibarsa sata ce, kuma za a iya gurfanar da mutum a kotu,” in ji Issa-Onilu.

Ya ce rushewar tarbiyya da rashin kulawar iyaye sun janyo irin wannan halayya, yana mai kiran shugabannin al’umma su gyara dabi’un jama'arsu.

Neja: Mutanen da suka mutu sun kai 42

Mun ruwaito cewa gobara ta tashi a ranar Talata, 21 ga Oktoba, 2025, bayan da tankar mai ta kife tare da fashewa a hanyar Bida–Badeggi–Agaie yayin da mazauna ke dibar mai.

Hukumar NEMA ta tabbatar da mutuwar mutum 42 — ciki har da mata 24, maza tara da yara tara — yayin da sama da 60 suka ji raunuka.

Jami’an ’yan sanda, DSS, NSCDC, FRSC da masu aikin gaggawa sun shiga aikin ceto, yayin da ake ci gaba da neman wasu da ba a gani ba.

Issa-Onilu ya ce NOA za ta ƙara kaimi wajen wayar da kai don hana dibar mai da kuma ƙarfafa martani na gaggawa a cikin al’umma idan irin hakan ta faru.

Kara karanta wannan

Kotu ta fadi dalilin dage zaman shari'ar kwamandojin 'Yan ta'addan Ansaru

Shugaban hukumar NOA ya ce za su kara kaimi wajen wayar da kan jama'a game da illar dibar mai daga tankar da ta fadi.
Shugaban hukumar NOA, Lanre Issa-Onilu, yana jawabi ga manema labarai a Abuja. Hoto: @NOA_Nigeria
Source: Facebook

Tinubu ya jajanta wa al'ummar jihar Neja

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya aika sakon ta'aziyya da jajantawa ga al'ummar jihar Neja fisa mutuwar mutane 42 a fashewar tankar mai.

Ministan yada labarai, Mohammed Idris ya fitar da sanarwar cewa Tinubu ya ce yana tare da iyalan da suka rasa 'yan uwansu a wannan mummunan iftila'i.

Domin jaddada kaduwarsa kan lamarin, Tinubu ya ba hukumar NOA da NEMa umarnin kai daukin gaggawa ga wadanda abin ya shafa, yayin da ya yi addu'a ga matattun.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com