Atiku da Wasu Manya na Fafutukar Fito da Shi, Shugaban IPOB Ya Rikita Lissafin Lauyoyi a Kotu

Atiku da Wasu Manya na Fafutukar Fito da Shi, Shugaban IPOB Ya Rikita Lissafin Lauyoyi a Kotu

  • Nnamdi Kanu ya raba gari da tawagar lauyoyinsa yayin da aka dawo zaman shari'arsa a babbar kotun tarayya mai zama a Abuja
  • Lauyoyin sun shaidawa kotu cewa Kanu ya datse aikinsu na kare shi, bisa haka suka nemi izinin alkali domin janyewa daga shari'ar
  • Mai Shari'a James Omotoshoya ya dage zaman shari'ar zuwa gobe Juma'a, 24 ga watan Oktoba, 2025 domin ba Kanu damar shiryawa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Najeriya – Shugaban ƙungiyar IPOB da aka haramta, Nnamdi Kanu, ya kori dukkan lauyoyinsa a lokacin zaman shari’arsa da ake ci gaba da saurare a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Bayan artabu mai zafi, sojoji sun dakile harin Boko Haram da ISWAP a jihohi 2

A zaman babbar kotun tarayya da ke Abuja yau Alhamis, Nnamdi Kanu ya bayyana wa alƙali cewa ya shirya kare kansa da kansa, ba tare da amfani da lauyoyi ba.

Jagoran IPOB, Nnamdi Kanu.
Hoton shugaban IPOB, Nnamdi Kanu a harabar kotu Hoto: @ayofel
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce bisa haka, dukkannin lauyoyi masu girma (SANs) da ke cikin tawagarsa ƙarƙashin jagorancin Kanu Agabi (SAN), sun janye daga ci gaba da wakiltarsa a shari’ar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan lamari dai na zuwa ne yayin manyan mutane ciki har da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar suka shiga fafutukar fito da Kanu.

Shugaban IIPOB zai kare kansa a kotu

Bayan janyewar su, Kanu ya mike daga cikin akwatin killace wanda ake tuhuma ya fara magana kai tsaye da kotu.

Jagoran kungiyar IPOB, wacce gwamnatin Najeriya ta ayyana matsayin kungiyar yan ta'adda, ya ƙalubalanci ikon kotun na ci gaba da sauraron karar da aka shigar a kansa.

Tun farko, babban lauyansa, Kanu Agabi (SAN) ya sanar wa kotu cewa duka manyan lauyoyin (SANs) da ke cikin tawagarsa, ciki har da Onyechi Ikpeazu, Paul Erokoro, Joseph Akubo, da Emeka Etiaba, sun janye daga wakiltar Kanu a shari’ar.

Kara karanta wannan

Nnamdi kanu: An gano abin da Buratai, gwamnoni da wasu manyan kasa za su fada a kotu

Agabi ya bayyana cewa dalilin janyewar su shi ne saboda “wanda ake tuhuma ya karɓe shari’ar hannunmu kuma muna girmama wannan shawara da ya yanke.”

Nnamdi Kanu ya sallami lauyoyinsa

Bayan wannan sanarwa, Mai Shari'a James Omotosho ya tambayi Kanu don tabbatar da maganar, kuma jagoran IPOB ya amsa da cewa ya shirya kare kansa da kansa.

Daga nan, alƙalin ya umarci duk sauran lauyoyin Kanu da ke cikin kotun su bar ɗakin shari’a nan take, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Bayan haka, Mai Shari'a Omotosho ya juya zuwa ga Kanu ya kuma bukace shi da ya fara gabatar da hujjojin kare kansa.

Sai dai Kanu ya fara kalubalantar hurumin kotun na ci gaba da shari’ar, amma kotu ta ƙi amincewa da hakan, ta kuma umarta shi da ya ci gaba da kare kansa.

Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu.
Hoton Nnamdi Kanu tare da jami'an tsaro a harabar kotu Hoto: @DSS
Source: Getty Images

An dage shari'ar Nnamdi Kanu

A wannan lokaci ne Onyechi Ikpeazu (SAN) ya sa baki, ya roƙi kotu ta ba Kanu ɗan lokaci domin ya shirya kare kansa, ganin cewa janyewar lauyoyin ta fara aiki ne da safiyar yau Alhamis.

Kara karanta wannan

Sowore: 'Yan sanda sun cafke tsohon dan takarar shugaban kasar Najeriya a kotu

Lauyan gwamnati bai yi musu da rokon ba, don haka Alƙali Omotosho ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar Juma’a, 24 ga Oktoba, domin ba wa Kanu damar fara kare kansa a hukumance.

ADC ta yi magana kan tsare shugaban IPOB

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta bayyana cewa ba ta dauki matsaya ba tukunna kan batun ci gaba da tsare jagoran kungiyar 'yan aware ta IPOB, Nnamdi Kanu.

Kakakin ADC na kasa, Bolaji Abdullahi ne ya bayyana haka a wata hira da aka yi da shi yayin da kiraye-kirayen a saki Kanu ke kara yawaita a Najeriya.

Haka kuma ya soki yadda jami’an tsaro suka yi amfani da karfi wajen tarwatsa masu zanga-zangar da ke neman a saki Nnamdi Kanu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262