Najeriya Ta Sake Martani kan Harajin Trump da Bukatar Karbar Baki daga Amurka

Najeriya Ta Sake Martani kan Harajin Trump da Bukatar Karbar Baki daga Amurka

  • Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, ya ce gwamnati ba za ta sake karɓar waɗanda Amurka ta ƙora ba
  • Ya bayyana cewa batun ya daina kasancewa abin tattaunawa na musamman tsakanin Najeriya da kasar Amurka
  • Tuggar ya ce Najeriya na maida hankali ne wajen inganta rayuwar ’yan ƙasarta, ba karɓar ’yan ƙasashen waje ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abu Dhabi – Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar, ya bayyana cewa Najeriya ba za ta karɓi waɗanda aka ƙora daga Amurka ba.

Ministan ya yi magana yana mai jaddada cewa batun ya daina zama jigo a huldar kasashen biyu daga yanzu.

Bola Tinubu|Donald Trump
Shugaba Bola Tinubu da Donald Trump na Amurka. Hoto: Bayo Onanuga|Getty Images
Source: Getty Images

The Guardian ta rahoto cewa Yusuf Tuggar ya yi wannan bayani ne yayin wata tattaunawa a wani taro da aka gudanar a birnin Abu Dhabi na UAE.

Kara karanta wannan

"Ba zan yi sulhu da yan bindiga ba," Gwamna ya shirya daukar jami'an tsaro 10,000

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce Najeriya ta bayyana matsayinta a fili, kuma yanzu ba ta ga dalilin da zai sa ta karɓi ’yan ƙasashen waje da aka turo da karfi daga ƙasashen waje ba.

Abin da Najeriya ta maida hankali a kai

Tuggar ya bayyana cewa manufar gwamnati ita ce mayar da hankali kan ci gaban al’ummar Najeriya, musamman wajen horar da matasa da samar da ayyukan yi.

Tsohon jakadan ya ce Najeriya na da yawan jama’a sama da miliyan 200 a yanzu, kuma ana sa ran zai kai miliyan 400 cikin shekaru 25 masu zuwa.

Dangantakar Najeriya/Amurka a yanzu

Tuggar ya bayyana cewa duk da wannan matsaya, dangantakar Najeriya da Amurka na tafiya cikin lumana da fahimtar juna.

Ya ce kin karɓar waɗanda aka ƙora daga Amurka ba wata matsala bace ta siyasa, illa dai tsarin da ke nuna fifikon Najeriya kan al’amuran cikin gida.

Ministan ya ce:

Kara karanta wannan

Ta yi tsami tsakanin fadar shugaban kasa, kungiyar CAN kan zargin kisan Kiristoci

“Abin da muke bukata shi ne a gina dangantaka mai girmama juna, ba irin wadda ke nuna rashin daidaito ba,”

Tuggar ya gargadi kasashe masu arziki

Ministan ya yi gargaɗi ga ƙasashe masu arziki, yana mai cewa bai kamata su riƙa kallon Afrika a matsayin fili ne kawai na samo albarkatun ƙasa ba.

Yusuf Maitama Tuggar
Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar. Hoto: @YusufTuggar
Source: Twitter

Ya kwatanta tsarin kasuwancin kasashe masu arziki da wasan kwamfuta na Minecraft, inda ’yan wasa ke hako ma’adinai, gina gine-gine da tara albarkatu ba tare da tsari ba.

“Wasu kasashe na kallon Afrika kamar wajen wasa ne: akwai mai, akwai gas, akwai ma’adinai, sai kawai su saka jari a nan suna kwashe ma'adinai. Wannan ba daidai ba ne,”

Inji Tuggar.

Martanin Najeriya kan harajin Trump

Ministan ya yi martani da aka tambayi Ministan kan harajin shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, wanda ke ɗaura 15% kan kayayyakin da ke fitowa daga Najeriya.

Rahoton CNB ya nuna cewa Tuggar ya ce Najeriya na da wasu dabaru da za su taimaka mata ta jure wannan matsin lamba.

Kara karanta wannan

'An fi kashe Musulmi,' Hadimin Trump ya karyata zargin kisan Kiristoci a Najeriya

Ya ce:

“Mu ƙasa ce mai girma wadda ke da mutane miliyan 230, don haka muna da babbar kasuwa ta cikin gida. Hakan kuma yana nufin muna da dimbin ƙwararru fiye da sauran ƙasashe.”

Kotun Amurka ta hukunta dan Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa wata kotun Amurka ta yanke wa wani dan Najeriya da ya yi aiki a kamfanin NNPCL hukunci.

Kotun ta gano Paulinus Okoronkwo ya karɓi $2.1m daga kamfanin mai na Addax ba bisa ka'ida a lokacin da ya ke aiki.

Bayan karbar kudin, kotun ta ce ya yi amfani da su wajen sayen katafaren gida a Amurka, wanda hakan ya jawo kwace kadarorinsa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng