Magana Ta Kare: Babban Hafsan Tsaro Ya Fadi Lokacin Kawo Karshen 'Yan Bindiga, Lakurawa
- Babban hafsan tsaro na kasa, Janar Christopher Musa, ya kai ziyarar ban girma zuwa gidan gwamnatin jihar Kebbi
- Janar Christopher Musa ya bada tabbacin cewa dakarun sojoji za su ci gaba da kara kaimi wajen kawo karshen 'yan bindiga da 'yan ta'addan Lakurawa
- Hakazalika babban hafsan tsaron ya yabawa gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris bisa irin goyon bayan da yake ba dakarun sojoji
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kebbi - Babban hafsan tsaro na kasa, Janar Christopher Musa, ya ba 'yan Najeriya tabbaci kan matsalar rashin tsaro.
Janar Christopher Musa ya tabbatarwa ’yan Najeriya cewa rundunar sojoji za ta ci gaba da kai farmaki domin kawar da ’yan ta’adda, ’yan bindiga, da Lakurawa daga sassan kasar nan.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta ce Janar Christopher Musa ya bayar da wannan tabbaci ne yayin da ya jagoranci manyan jami'an sojoji wajen ziyarar ban girma ga Gwamna Nasir Idris a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi.

Kara karanta wannan
"Ba zan yi sulhu da yan bindiga ba," Gwamna ya shirya daukar jami'an tsaro 10,000
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yaushe za a kawo karshen 'yan bindiga?
Babban hafsan tsaron ya bada tabbacin cewa nan bada jimawa ba dakarun sojoji za su kawar da masu aikata laifuffuka musamman 'yan bindiga, Lakurawa da sauransu.
“Muna sane da ayyukan ’yan ta’adda da Lakurawa a yankin Arewa maso Yamma da kuma irin kokarin da Gwamna Idris da takwarorinsa ke yi wajen tallafa wa dakarunmu da kayan aiki domin su fuskanci maharan duk lokacin da suka kai hari ga fararen hula. Wannan abin a yaba ne."
“Don haka, Mai girma gwamna, muna bukatar ci gaba da irin wannan goyon baya domin mu kawar da wadannan ’yan ta’adda daga kasa baki daya.”
- Janar Christpher Musa
Janar Christopher Musa ya kuma bukaci gwamnatin jiha da al’ummar Kebbi su rika taimaka wa dakarun tsaro da bayanai game da inda ’yan ta’adda suke boyewa ko inda suke kai hare-hare, domin taimakawa wajen gudanar da ayyukan tsaro cikin gaggawa.
Gwamna Nasir ya yabawa hafsan tsaro
A nasa bangaren, Gwamna Nasir Idris ya godewa Janar Christopher Musa bisa halartar taron majalisar sarakunan gargajiya na Arewa, da aka gudanar a Kebbi da kuma ziyarar ban girma da ya kai gidan gwamnati.

Source: Facebook
Gwamnan ya yabawa babban hafsan tsaron da sauran hafsoshin sojoji bisa irin rawar da suke takawa wajen kare rayukan jama’a da dukiyoyin su a jihar da fadin kasar nan.
Ya kuma yaba da yadda babban hafsan tsaron da babban hafsan rundunar sojojin sama suka gaggauta kafa sansanonin sojoji a yankunan da ake fama da matsalolin tsaro a jihar Kebbi.
“Gwamnatina za ta ci gaba da bai wa rundunar sojoji cikakken goyon baya a dukkan hanyoyin da za su taimaka wajen kawar da matsalar ’yan bindiga da sauran masu aikata laifuffuka a fadin kasa."
- Gwamna Nasir Idris
Sojoji sun fafata da 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun yi arangama da wasu miyagun 'yan bindiga a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan
Jam'iyyar ADC ta kori mataimakin shugaba da wasu manyan jami'ai 8, an fadi dalili
'Yan bindigan sun shiryawa sojojin kwanton bauna ne domin ramuwar gayya kan kisan da aka yi wa wani tantirin jagoran 'yan ta'adda.
Sojojin sun yi nasarar fatattakar 'yan bindigan tare da raunata da dama daga cikinsu bayan an dauki lokaci ana artabu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
