Sakon Nadin Sabon Minista Ya Isa Majalisar Dattawa, Akpabio Ya Karanta Wasikar Tinubu
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tura sunan Dr. Bernand Mohammed Doro ga Majalisar Dattawa domin tantance shi a matsayin Minista
- Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya karanta wasikar Bola Tinubu a zaman yau Laraba, 22 ga watan Oktoba, 2025
- Tinubu ya nada sabon ministan ne biyo bayan murabus din Farfesa Nentawe Yilwatda wanda ya zama shugaban APC na kasa a watan Yuli
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Najeriya – Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rubuta wasika zuwa ga majalisar dattawa yana neman a tabbatar da nadin Dr. Bernard Mohammed Doro daga jihar Filato a matsayin Minista.
Nadin Mohammed Doro na zuwa ne bayan APC ta zabi Farfesa Nentawe Yilwatda a matsayin shugabanta na kasa a watan Yuli, wanda haka ya sa ya yi murabus daga kujerar Ministan jin kai.

Source: Facebook
Jaridar The Cable ta tattaro cewa a jiya Talata, Tinubu ya sanar da nadin Doro domin maye gurbin Farfesa Nentawe daga jihar Filato.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya mika sunan Minista Majalisa
Wasikar nadin sabon ministan ta isa Majalisa Dattawa a zaman yau Laraba, kuma shugaban Majalisar, Sanata Godswill Akpabio ya karanta ga sauran sanatoci.
Wasikar ta nuna cewa Shugaba Tinubu ya yi nadin ne bisa tanadin sashe na 147(2) na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 da aka yi wa gyara.
Wasikar ta ce:
“Dogaro da tanadin sashe na 147(2) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 da aka yi wa gyara, ina farin cikin turo wa majalisar dattawa sunan Dr. Bernard Mohammed Doro domin tabbatar da shi a matsayin Minista.
"Ina fatan wannan bukata za ta samu kulawa da saurin amincewa kamar yadda kuka saba, tare da tabbatar da girmamawa ta gare ku, mai girma shugaban majalisa da sanatoci masu daraja.”
Majalisar Dattawa za ta tantance Minista
Bayan karanta wasikar, Sanata Akpabio ya mika bukatar ga kwamitin duka majalisar domin yin nazari da bayar da rahoto.
Ya ce, “An mika wannan bukata ga kwamitin Majalisa gaba daya domin nazari, kuma za a mayar da rahoto ga wanda ya turo sakonnnadin da zarar an gama aikin.”
Ana sa ran dai Majalisar za ta sanya ranar tantance Dr. Bernard Mohammed Doro, wanda zai bayyana a gabanta kamar yadda doka ta tanada, cewar The Nation.
Bayan kammala tantance shi, Majalisar za ta yanke shawarar amince wa da nadinsa ko akasin haka, sannan ta tura wa Shugaban Kasa matakin da ta dauka.

Source: Facebook
An yi cacar baki tsakanin Akpabio da Natasha
A wani labarin, kun ji cewa an yi muhawara mai zafi a zaman majalisar dattawan Najeriya na ranar Talata, 21 ga watan Oktoba, 2025 kan kudirin gyaran dokar zubar da ciki.
An tattaro cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio da Sanata Natasha Akpoti sun yi ce-ce-ku-ce a Majalisa bayan dakatar da tattaunawa kan dokar.
Bayan zaman majalisar, Sanata Akpoti-Uduaghan ta bayyana bacin ranta saboda hana ta yin magana kan kudirin, wanda ta ce ya shafi mata da lafiyarsu kai tsaye.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


