Wa Ya Kashe Ta? Mahaifin Ƴar Jarida da Ta Mutu a Abuja Ya Aika Sako ga Ƴan Sanda
- Ifeanyi Maduagwu, mahaifin 'yar jarida Somtochukwu Maduagwu, ya dage cewa an kashe masa ’yarsa ne da gangan a Abuja
- An rahoto cewa ’yar jaridar ta Arise TV ta rasu bayan harin ’yan fashi a gidanta da ke Katampe, Abuja, a daren 29 ga Satumba, 2025
- Yayin da ake zargin ko ita ce da kanta ta yi silar ajalinta, Mr. Ifeanyi ya ce sam bai yarda ba, inda ya aika sako ga 'yan sanda
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Mahaifin Somtochukwu Maduagwu, 'yar jarida da ke aiki da Arise TV, ya karyata rahotannin da ke cewa ’yarsa ta mutu ne bayan faɗowa daga bene yayin tsere wa ’yan fashi.
Sananniyar 'yar jaridar, wacce aka fi kira da Sommie, ta mutu ne a daren ranar 29 ga Satumba bayan 'yan fashi sun farmaki gidanta da ke Katampe, a Abuja.

Kara karanta wannan
'Dan Najeriya ya yi amfani da kayan aikin mace, ya burma kansa a matsala a Ingila

Source: Twitter
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Kashe 'diya ta aka yi" - Mahaifin 'yar jarida
A wata hira da BBC Igbo, Mr. Ifeanyi Maduagwu, ya ce labarin da ake yadawa ba gaskiya ba ne, yana mai cewa alamu sun nuna cewa an kashe ta ne da gangan.
“Ba zan taɓa yarda cewa Sommie ta yi ƙoƙarin tserewa ta hanyar durowa daga bene mai hawa uku ba. Wannan labari ba gaskiya ba ne. Ina da tabbacin cewa kashe ’ya ta aka yi,” in ji Ifeanyi.
Ya ƙara da cewa ’yarsa tana matukar tsoron yin tsalle ko da kuwa tsalle ne daga kan tebur, balle kuma daga bene mai hawa uku.
“Ina roƙon ’yan sanda su gudanar da cikakken bincike domin a gano gaskiyar abin da ya faru."
- Mr. Ifeanyi Maduagwu.
Yanayin da 'yar jaridar ta mutu
A daren 29 ga Satumba, 2025, wasu ’yan fashi da makami sun kai hari gidan 'yar jaridar da ke Katampe, Abuja, inda suka harbe mai gadin gidan, Barnabas Danlami, har lahira.
Rahotanni sun ce Somtochukwu ta faɗo daga bene yayin gudun tsira, amma mahaifinta ya ce wannan labari an ƙirƙire shi ne don ɓoye gaskiya.
Ya kuma yi zargin cewa an ƙi taimaka mata da wuri, inda asibitin da aka kai ta ya jinkirta ba ta kulawa saboda sai an ba su wasu takardu.

Source: Twitter
’Yan sanda sun kama mutum 12
Rundunar ’yan sandan babban birnin tarayya (Abuja) ta tabbatar da cewa ta kama mutum 12 da ake zargi da hannu cikin harin.
Wadanda aka kama sun haɗa da Shamsudeen Hassan, Hassan Isah, Abubakar Alkamu, Sani Sirajo, Mashkur Jamilu, Suleiman Badamasi, Abdulsalam Saleh.
Sannan akwai Zaharadeen Muhammad, Musa Adamu, Sumayya Mohammed, Isah Abdulrahman, da Musa Umar.
Kwamishinan ’yan sanda na Abuja, Ajao S. Adewale, ya ce an kama su ne ta hanyar binciken fasahar zamani da tattara bayanan sirri.
Daya daga cikin wadanda ake zargi, Shamsudeen Hassan, ya amsa cewa shi ne ya harbi mai gadin gidan, yayin da bincike ya gano cewa suna samun makamai daga Jamhuriyar Nijar.
Kalli tattaunawar a nan kasa:
Tinubu ya magantu kan kisan 'yar jarida
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa wata fitacciyar yar jarida a birnin tarayya, Abuja.
Tinubu ya jajanta wa iyalan marigayiya Somtochukwu Maduagwu, mai gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin Arise News, wacce aka kashe a daren 29 ga Satumba, 2025.
Shugaban kasar ya umurci jami’an tsaro da su gudanar da bincike cikin gaggawa don kamo wadanda suka aikata wannan mummunan aiki kan matashiyar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

