Zubar da Cika: Sanata Akpabio da Natasha Sun Yi Cacar Baki a Majalisar Dattawa
- Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da Sanata Natasha Akpoti sun yi ce-ce-ku-ce a Majalisa kan kudirin dokar zubar da ciki
- Rahotanni sun nuna cewa yan Majalisar Dattawa sun yi mahawara mai zafi kan kudirin, lamarin da ya sa Akpabio ya jingine shi
- Sai dai Sanata Natasha ta nuna bacin ranta bisa hana ta magana duk da cewa kudirin ya shafi mata ne kai tsaye
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Najeriya – An yi muhawara mai zafi a zaman majalisar dattawan Najeriya ranar Talata kan kudirin gyaran dokar zubar da ciki.
Rahoto ya nuna cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya sun yi ka-ce-na-ce nan kudirin.

Source: Facebook
Me kudirin dokar zubar da ciki ya kunsa?
The Cable ta rahoto cewa kudirin dokar na neman ƙara tsaurara hukunci ga duk wanda aka kama da laifin taimakawa ko shirya zubar da ciki a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A karkashin kudirin, wanda ke ba da magani ko kayan aikin zubar da ciki zai fuskanci hukuncin shekaru 10 a gidan yari ba tare da zabin tara ba, maimakon shekaru uku a baya.
Sai dai muhawarar ta yi zafi lokacin da sanatoci suka kasa tsaida matsaya kan zubar da cikin, wasu na ganin akwai lokacin da ya halatta a zubar.
Akpabio ya hana Sanata Natasha magana
Bayan muhawara ta yi zafi, Akpabio ya dakatar da tattaunawa kan kudirin, ya umarci kwamitin shari’a, haƙƙin ɗan adam da harkokin doka da su sake nazarin sassan da ake cece-kuce a kansu su kawo rahoto cikin mako biyu.
Sanatoci sun amince da shawarar ta hanyar kuri’ar murya, amma duk da haka Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta ɗaga hannu tana neman a ba ta dama ta yi magana.
Sai dai Sanata Godswill Akpabio ya amsa mata da cewa “an dakatar da batun gaba ɗaya.”
Nan take, Sanata Adams Oshiomhole daga Edo ta Arewa ya tashi ya kawo hujjar cewa ba Natasha damar ta yi magana bayan an rufe tattaunawa ya saba wa dokar majalisa.
Akpabio ya goyi bayan hujjar Oshiomhole bisa dokar majalisa ta sashe na 52, sakin layi na 6, wanda ke hana komawa ga batu da aka gama tattaunawa a kai.

Source: Facebook
Sanata Natasha ta nuna bacin ranta
Bayan zaman majalisar, Sanata Akpoti-Uduaghan ta bayyana bacin ranta saboda hana ta yin magana kan kudirin, wanda ta ce ya shafi kai tsaye haƙƙin mata da lafiyarsu.
A rahoton Vanguard, Natasha ta ce:
“Na ji takaici saboda ba a ba ni damar magana kan batu da ya shafi mata kai tsaye ba. Ni mace ce, uwa ce, kuma na ji cewa kamata ya yi a ba ni dama in yi magana, saboda mu biyu ne kawai mata a majalisar yau, ni da Sanata Banigo.”
Majalisa ta amince da nadin shugaban NPC
A wani rahoton, kun ji cewa Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin Dr. Aminu Yusuf daga jihar Neja a matsayin sabon shugaban hukumar kidaya ta kasa watau NPC.
Wannan tabbaci ya biyo bayan gabatar da rahoton kwamitin majalisar kan shaidar dan kasa da kidaya, wanda Sanata Victor Umeh daga jihar Anambra ya aiwatar.
Bugu da kari, Majalisar ta kuma amince da nadin Joseph Haruna Kigbu da Tonga Betara Bularafa a matsayin kwamishinoni a NPC.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


