Magana Ta Girma: Sarakuna Sun Tsoma Baki kan Zargin Akpabio da Kisan Kai
- Sarakunan gargajiya a Akwa Ibom sun shiga lamarin da ke faruwa bayan zargin Sanata Godswill Akpabio da kisan kai
- Dattawan a jihar sun bai wa Patience Akpabio da mijinta Ibanga Akpabio wa’adin kwanaki 7 su bayyana gaban su kan zargin batanci ga Akpabio
- Sarakunan sun ce Patience Akpabio ta yi amfani da kalmomin rashin kunya a kafar sadarwa inda ta zargi Sanatan da hannu a kashe-kashe
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Uyo, Akwai Ibom - Majalisar sarakunan gargajiya ta Annang a Jihar Akwa Ibom ta shiga lamarin da ke faruwa da Sanata Godswill Akpabio.
Majalisar sarakunan wato Afe Nkuku Annang, ta bukaci Patience Akpabio, ‘yar uwar matar Godswill Akpabio, da mijinta Ibanga Akpabio, su bayyana a gaban ta.

Source: Facebook
Sarakuna sun bukaci zama da surukar Akpabio
Rahoton Punch ya ce sarakunan sun ba su wa'adin ne su bayyana gabansu cikin kwanaki bakwai domin amsa tambayoyi da kuma dalilin kalamai da zarge-zarge kan Akpabio.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana tuhumarta ne kan wasu kalaman batanci da ta wallafa a kafafen sada zumunta da ke zargin Akpabio da kashe-kashe a lokacin da yake gwamna.
A wata sanarwa da aka fitar bayan taronsu, sarakunan sun nuna damuwa kan kalaman da suka kira na rashin kunya da cike da kazafi da Patience Akpabio ta yi.
Majalisar ta ce ba za ta lamunci irin wannan abin kunya daga mace da aka aurar a cikin zuri’ar Annang ba, musamman daga iyalin Akpabio na Essien Udim.

Source: Facebook
Barazanar da sarakuna suka yiwa surukar Akpabio
Har ila yau, majalisar ta jaddada cewa rashin bayyana gaban su cikin wa’adin kwanaki bakwai zai haifar da hukunci mai tsanani bisa al’ada domin zama izina ga wasu da ke shirin yin irin haka a gaba.
Sarakunan sun kuma ce idan tana da wata matsala ta gida ko ta siyasa, ya kamata ta kai koke ta hanyoyin doka ko ta dattawan iyalai, maimakon cin mutunci da zage-zage a kafafen sada zumunta, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan
Jam'iyyar ADC ta kori mataimakin shugaba da wasu manyan jami'ai 8, an fadi dalili
Sun kuma bayyana cewa kalaman nata sun jawo tozarci ga Sanata Akpabio da kuma Gwamna Umo Eno, suna mai cewa dukkan zarge-zargen da ta yi “marasa tushe ne kuma da ba su da kan gado.”
A karshe, majalisar ta ce ta tsarkake sunayen Akpabio da Gwamna Eno daga dukkan zarge-zargen da Patience ta yada, tare da gargadin cewa ba za ta lamunci irin wannan rahin kunya ga dattijon Annang ba.
2027: Akpabio ya yi albishiri ga Tinubu
Mun ba ku labarin cewa shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya sanar da Bola Tinubu abin da bai sani ba kan shirin wasu gwamnonin jam'iyyun adawa.
Sanata Godswill Akpabio ya fadawa shugaban kasar cewa wasu gwamnonin jam'iyyun adawa sun shirya dawowa cikin jam'iyyar APC domin ba shi karfi a zaben 2027 da ke tafe.
Shugaban majalisar dattawan ya kuma bayyana cewa 'yan Najeriya sun fara gani a kasa kan manufofin da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa bayan daukar wasu matakai masu tsauri.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
