Za a Dauke Wutar Lantarki na Kwanaki 10, An Lissafa Yankuna 25 da abin Zai Shafa
- Kamfanin rarraba wuta na MainPower (MEDL) ya sanar da daukewar wuta na tsawon kwana 10 wasu yankuna takwas na Enugu
- Aikin zai shafi layukan wutar lantarki da dama daga ranar 22 zuwa 31 ga Oktoba, 2025, tsakanin 9:00 na safe zuwa 5:00 na yamma
- Kamfanin MEDL ya nemi afuwa daga jama’a, yana mai cewa aikin zai inganta rarraba wutar lantarki a yankin gaba ɗaya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Enugu - Kamfanin rarraba wuta na MainPower (MEDL) ya sanar da cewa za a samu katsewar wutar lantarki na tsawon kwana 10 a wasu yankuna na jihar Enugu.
A cewar kamfanin MEDL, dauke wuta a wadannan yankuna ya zama wajibi domin gudanar da manyan ayyukan gyare-gyare da kula da kayan wutar lantarki.

Source: Getty Images
Shugaban sashen yada labarai na kamfanin, Mista Emeka Ezeh, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Talata, inji rahoton The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce aikin gyaran zai gudana ne a tashar kamfanin TCN da ke New Haven, kuma aikin zai inganta karfin wutar lantarki da rage matsalolin katsewar wuta a birnin Enugu.
Layukan wutar lantarki da aikin zai shafa
A cewar Ezeh, aikin zai kasance cikin tsari, inda za a rika rufe wasu layukan wuta a ranaku daban-daban daga Laraba, 22 ga Oktoba, zuwa Alhamis, 31 ga Oktoba, 2025, tsakanin karfe 9:00 na safe zuwa 5:00 na yammacin kowace rana.
Yankunan da abin zai shafa sun haɗa da:
- Kingsway Line 1 (22 ga Oktoba)
- Emene Industrial Line 1 (23 ga Oktoba)
- Thinkers Corner Line (24 ga Oktoba)
- Trans Ekulu Line (25 ga Oktoba)
- Kingsway Line 2 da 9th Mile Line (26 ga Oktoba)
- Emene Industrial Line 2 (28 ga Oktoba)
- Ugwuogo Line (29 ga Oktoba)
- Ituku Ozalla Line (31 ga Oktoba)
Yankunan da za a dauke wa wutar lantarki
A cewar kamfanin, yankunan da za su fi fuskantar katsewar wutar sun haɗa da:
Emene Industrial Layout, Abakpa Nike, Trans-Ekulu, Thinkers Corner, Ugbo Nnebedum, Nkpologwu, 9th Mile, Shoprite, Golf Estate, Zoo Estate, Okpara Avenue, da Nowas.
Haka kuma, wasu yankunan kamar Kingsway Road, Abakaliki Road, CBN Quarters, Railway Quarters, Coal Camp, Uwani, Asata, Golden Royale, Iva Valley, Centenary City, Ugwuaji, Amechi, da Obeagu za su fuskanci rashin wuta a lokacin aikin.

Source: Original
Kamfanin lantarki ya nemi afuwa daga jama’a
Kamfanin MEDL ya nemi afuwar jama'a da fahimtarsu game da wannan aiki, yana mai cewa aikin zai kawo babban sauyi wajen inganta samar da wuta da dorewarta a yankin, inji rahoton Punch.
“Muna matukar nadamar katsewar wutar da za a fuskanta, amma aikin yana da muhimmanci domin tabbatar da ci gaba da rarraba wutar lantarki a Enugu.”
- Mista Emeka Ezeh.
Ya kara da cewa bayan kammala aikin, za a samu karuwar wutar lantarki da tsaro a tsarin rarraba wuta a yankin.
An samu lalacewar tushen wutar lantarki
A wani labarin, mun ruwaito cewa, an sake samun lalacewar tushen wutar lantarki na Najeriya, a safiyar ranar Laraba, 10 ga watan Satumba, 2025.
Kamfanin rarraba wuta na Abuja (AEDC) ya fitar da sanarwar lalacewar tashar, wanda ta ce ya jawo katsewar wuta a yankunan da yake kula da su.
An rahoto cewa, karfin wutar lantarki ya ragu ya ragu daga 2,917.83MW zuwa 1.5 MW kacal tsakanin ƙarfe 11:00 na safe zuwa 12:00 na rana.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


