Kanu: Dan Ta'addan da Aka Rike Ya Jero Gwamnoni, Ministocin Tinubu, Buhari a Shaidu

Kanu: Dan Ta'addan da Aka Rike Ya Jero Gwamnoni, Ministocin Tinubu, Buhari a Shaidu

  • Jagoran haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu ya amince da fara kare kansa a kotu bayan zanga-zangar neman sakin sa
  • Nnamdi Kanu ya sanar da kotun tarayya cewa zai kira mutane 23 a matsayin shaidu ciki har da ministoci da tsofaffin hafsoshin soja
  • Haka zalika Kanu ya bukaci a ba shi kwanaki 90 domin kammala kare kansa tare da gabatar da bayanin gaskiya daga bakinsa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Jagoran kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, ya bayyana shirin fara kare kansa a gaban kotu bayan wata zanga-zanga da aka yi a Abuja domin neman a sake shi.

Wannan mataki na Kanu ya biyo bayan ƙin amincewar kotu da ƙarar da ya shigar don kalubalantar hurumin wani alkali kan ci gaba da shari’arsa.

Kara karanta wannan

Zaben Kamaru: Matasa sun barke da zanga zanga, an yi arangama da 'yan sanda

Shugaban IPOB, Kanu
Shugaban 'yan ta'addan IPOB, Nnamdi Kanu. Hoto: Omoyele Sowore
Source: Twitter

Zagazola Makama ya wallafa cewa Kanu ya fadi haka ne a cikin sabuwar takardar da ya mika wa kotu ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kanu ya ce ya shirya kare kansa bisa umarnin kotun da ta bukaci ya fara karewa daga ranar 24, Oktoban 2025.

Nnamdi Kanu zai kira shaidu 23 a kotu

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Kanu ya sanar da mai shari’a James Omotosho cewa zai gabatar da shaidu 23.

Ya ce shaidun za su bayar da muhimman bayanai kan lamuran da suka shafi zarge-zargen da ake masa, kuma zai bayar da hujjoji daga bakinsa domin bayyana ainihin abin da ya faru.

Ya roki kotu ta ba shi kwana 90 domin kammala kare kansa bisa ga yawan shaidu da zai kira da kuma muhimmancin bayanan da za su bayar.

Jerin shaidun da Kanu ya bayyana

A cikin jerin da ya gabatar wa kotu, Kanu ya ce zai kira tsohon ministan tsaro Janar Theophilus Danjuma (mai ritaya), tsohon hafsan sojoji Janar Tukur Buratai (mai ritaya).

Kara karanta wannan

Magana ta kare: Kotun Koli ta shirya raba gardama kan dokar ta bacin da Tinubu ya sa a Rivers

Haka zalika zai gabatar da gwamnonin jihohi Babajide Sanwo-Olu na Legas da Hope Uzodinma na Imo.

Ya kuma hada da ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ministan ayyuka Dave Umahi, da tsohon gwamnan Abia, Okezie Ikpeazu.

Ministan Abuja, Nyesom Wike
Ministan Abuja da Kanu ya ambata a matsayin shaida. Hoto: Nyesom Ezonwo Wike
Source: Facebook

Sauran sun hada da tsohon ministan shari’a Abubakar Malami, tsohon shugaban hukumar leken asiri ta kasa (NIA) Ahmed Rufai Abubakar, da kuma tsohon shugaban DSS, Yusuf Magaji Bichi.

Shugaban IPOB ya shirya kare kansa a kotu

Jagoran IPOB ya ce manufarsa ita ce tabbatar da adalci ta hanyar da komai zai bayyana filla-filla kan zargin da aka masa.

Kanu ya yi magana yana mai cewa:

“Zan tabbatar da cewa ba za a bata lokaci a kotu ba, domin kowa ya ga an yi adalci kuma an bayyana gaskiya.”

An kama mutanen Kanu yayin zanga-zanga

A wani labarin, mun kawo muku cewa 'yan sanda sun kama Aloy Ejimakor, wanda shi ne lauya na musamman ga Nnamdi Kanu da wasu mutane 12.

An kama su ne bayan zanga-zangar neman a saki Kanu, kuma an tuhume su da laifuka da suka hada da hada baki da bijirewa doka.

Kara karanta wannan

Sowore: An firgita masu zanga zanga, an kama mutanen Nnamdi Kanu a Abuja

Omoyele Sowore da ya jagoranci zanga zangar ya ce 'yan sanda sun lakada musu duka kafin su tafi da su caji ofis a birnin tarayya Abuja.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng