"Yara sama da 100,000 na cikin Barazana": Manyan Arewa Sun Waiwayi Almajirai

"Yara sama da 100,000 na cikin Barazana": Manyan Arewa Sun Waiwayi Almajirai

  • Masana da jami’an tsaro sun bayyana tsarin almajiranci da ake amfani da shi a yanzu a matsayin bama-bamai a tsakanin al'umma
  • An bayyana cewa fiye da yara 100,000 na yawo a tituna cikin rashin kulawa da barazanar fadawa hannun miyagu
  • Wannan matsala ta ja hankalin masu ruwa da tsaki a jihar Sakkwato, inda ta bukaci a zauna wuri guda domin gyara tsarin almajirai

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Sokoto – Masu ruwa da tsaki a jihar Sakkwato sun nemi a gudanar da cikakken gyara na tsarin Almajiri domin ceto rayuwar yara.

A wani zama da aka yi a jihar Sakkwato, an yi gargadin cewa yawaitar yara masu bara a tituna na zama barazana babba ga tsaron Najeriya da ma yankin Arewa baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An gano masu yayata 'labarin kisan kiristoci' a Najeriya

Ana son inganta tsarin karatun almajiri
Taswirar jihar Sakkwato da aka taru a kan almajirai Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Punch ta wallafa cewa an tattauna wannan matsala ne a wani taro da aka shirya a ranar Litinin, karkashin Sokoto Advancement Forum (SAF).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gano matsalar yawon bara a Arewa

Mahalarta taron sun hada da masana ilimi, jami’an tsaro, da manyan jami’an gwamnati, kuma sun bayyana lamarin yara kan tituna a matsayin bama-bamai masu jiran fashewa.

Mataimakin shugaban SAF kuma tsohon shugaban Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Farfesa Riskuwa Shehu, ya ce an shirya taron domin samar da hanyoyin magance bara.

Ya bayyana cewa ana fatan kawo karshen yawon da yara ke yi a tituna, tare da shigar da su cikin tsarin ilimi addini da zamani.

Ya ce:

“Mun tattauna hanyoyin magance barace-barace, yawo a titi, da kuma irin hadurran da yara ke fuskanta. Wannan tsarin da ake kira Almajiranci, a halin yanzu, yana tauye wa yara damar rayuwa, ilimi da kima."

Ya kara da cewa, bisa binciken da aka yi, jihar Sakkwato na daya daga cikin jihohin da ke da mafi yawan yaran almajirai a Najeriya.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kashe hatsabibin dan bindiga Abu AK da ya shiga gari cin kasuwa

Ana ganin cewa yaran da ke almajirci a Sakkwato sun kai tsakanin 100,000 zuwa 400,000, duk suna rayuwa cikin talauci da rashin kulawa.

Gwamnati na aiki don kare yara

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Sakkwato, Ahmad Musa, ya bayyana cewa tsarina almajiri ya zama babban barazana ga tsaro.

Gwamnatin Sakkwato na aiki don kare yara
Hoton gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sakkwato Hoto: Ahmed Aliyu 2023
Source: Facebook

Ya ce yara da ke yawo a tituna na fadawa hannun kungiyoyin ta’addanci da miyagu a cikin sauki saboda ba sa kusa da magabatansu.

Ya ce:

“Wannan tsarin yana haddasa daukar yara cikin kungiyoyin yan ta'adda da miyagun kungiyoyi. Idan ba a gyara ba, zai ci gaba da haifar da yara da ke kallon laifi a matsayin hanyar rayuwa."

Kwamishinonin Harkokin Addini da Ilimi, Dr. Jabir Maihula da Farfesa Ladan Ala, sun tabbatar da kudurin gwamnatin jihar na gyara tsarin Almajiri.

Sun bayyana cewa akwai burin hada makarantu na Qur’ani da tsarin ilimin boko, da kuma tallafa wa iyalai domin inganta rayuwar yara.

Yadda almajiri ya zama shugaban NNPCL

A baya, mun wallafa cewa tsohon shugaban kamfanin man fetur na ƙasa, NNPCL, Mele Kyari, ya bayyana yadda ya fara rayuwarsa a matsayin ɗalibin makarantar tsangaya.

Kara karanta wannan

Ana fargabar mutane da yawa sun mutu da wata tanka ta yi bindiga a Najeriya

A yayin da yake murnar cika shekaru 60 da haihuwa — a kalandar Musulunci — Kyari ya nuna godiyarsa ga Najeriya bisa damar da ya samu daga matakin farko har zuwa wannan matsayi.

Ya kuma jaddada cewa wannan nasara ba ta samu cikin sauƙi ba, domin ya sha wahalhalu, gazawa, nasarori da ƙalubale tun a lokacin da ya ke almajiri a tsangaya har ya girma.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng