Nnamdi Kanu: ADC Ta Fadi Matsayarta kan Tsare Jagoran Kungiyar IPOB
- Jam'iyyar ADC mai hamayya ta yi tsokaci kan batun ci gaba da tsare jagoran kungiyar 'yan aware ta IPOB, Nnamdi Kanu
- Mai magana da yawun ADC ya bayyana cewa lamarin Nnamdi Kanu har yanzu yana gaban kotu kan tuhume-tuhumen da gwamnati ke yi masa
- Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa jam'iyyar za ta jira ta ga yadda shari'ar jagoran na IPOB za ta kaya a gaban kotu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta yi magana kan batun tsare jagoran kungiyar 'yan aware ta IPOB, Nnamdi Kanu.
Mai magana da yawun ADC, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa jam’iyyar ba ta yi wata matsaya ba, kan ci gaba da tsare Nnamdi Kanu.

Source: Twitter
Bolaji Abdullahi ya bayyana haka ne yayin wata tattauna cikin shirin ‘Politics Today’ na Channels Tv a ranar Talata, 21 ga watan Oktoban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
ADC na goyon bayan zanga-zangar Nnamdi Kanu
Ya soki yadda jami’an tsaro suka yi amfani da karfi wajen tarwatsa masu zanga-zangar da ke neman a saki Nnamdi Kanu.
Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa matsayar jam’iyyar ADC tana kan kare ’yancin ’yan kasa na yin zanga-zanga cikin lumana.
"Ba tare da tsoma baki kan dalilin da ya sa ake tsare da Nnamdi Kanu ba, jam’iyyarmu ba ta fitar da wata sanarwa a kai ba."
"Abin da muke fada shi ne cewa ’yan kasa na da cikakken ’yanci na yin zanga-zanga, ko don goyon bayan abin da gwamnati ta yi ko adawa da abin ta yi. Wannan yanci ginshikin dimokuradiyya ne kuma dole ne a mutunta shi.”
- Bolaji Abdullahi
Me ADC ta ce kan tsare Nnamdi Kanu?
Bolaji Abdullahi ya ce jam’iyyar ba za ta yi tsokaci kai tsaye kan tsare Nnamdi Kanu ba saboda shari’arsa na gaban kotu.
"Ba a yankewa Nnamdi Kanu hukunci ba tukuna, kuma tunda shari’ar tana a gaban kotu, ba za mu yi wani sharhi kai tsaye ba."
"Idan an same shi da laifi ne, sannan za mu iya tattaunawa kan dalilin da yasa aka sako wasu masu laifi da masu safarar miyagun kwayoyi, yayin da ake rike da shi."
- Bolaji Abdullahi

Source: Facebook
Bolaji Abdullahi ya kuma soki matakin hana masu zanga-zanga shiga harabar majalisar dokoki ta kasa yana mai cewa hakan ya sabawa tsarin dimokuradiyya.
"Majalisar dokoki ita ce cibiyar dimokuradiyya a Najeriya. Abin mamaki ne ganin cewa ana hana masu zanga-zanga zuwa can."
"Yan kasa na da ’yanci su shiga, su mika wasiku ko korafe-korafe ga wakilansu, wannan shi ne ma’anar dimokuradiyya."
- Bolaji Abdullahi
Atiku ya magantu kan Nnamdi Kanu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimajin shugaban kasan Najeriya, Atiku Abubakar, ya yi magana kan ci gaba da tsare Nnamdi Kanu.
Atiku Abubakar ya bayyana cikakken goyon baya ga fafutukar 'yancin jagoran kungiyar ta'addanci (IPOB), Nnamdi Kanu.

Kara karanta wannan
Jam'iyyar PDP da sakatarenta na ƙasa sun samu sabani kan takardar da aka aika wa INEC
Tsohon mataimakin shugaban kasan ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta saki, Mazi Nnamdi Kanu, ko kuma gurfanar da shi gaban kotu bisa tsarin doka.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

