ASUU Ta Janye Yajin Aiki a Jami'o'i, Ta Kafa wa Gwamnatin Tinubu Sharadi
- Ƙungiyar ASUU ta dakatar da yajin aikin gargadi na makonni biyu da ta fara a ranar 13, Oktoba, 2025
- Ta ce gwamnati na da wata ɗaya kacal don cika bukatunta da suka shafi yarjejeniyar 2009 da sauran hakkoki
- ASUU ta yi gargadi da cewa za ta koma yajin aiki ba tare da sanarwa ba idan ba a ɗauki mataki ba kan bukatunta
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa, ASUU, ta sanar da dakatar da yajin aikin gargadi na makonni biyu da ta fara a ranar 13, Oktoba, 2025.
Wannan mataki na zuwa ne bayan tattaunawa da gwamnatin tarayya da majalisar dokoki ta ƙasa kan cika wasu daga cikin bukatun ƙungiyar.

Source: Twitter
Rahoton Channels TV ya ce shugaban ƙungiyar, Farfesa Chris Piwuna, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farfesa Chris Piwuna ya ce an yanke shawarar dakatar da yajin aikin ne saboda sababbin alkawura daga gwamnati.
ASUU ta ba gwamnati wa’adin wata 1
Farfesa Piwuna ya ce ASUU ta dakatar da yajin aikin ne saboda sahihin shirin da kwamitin Yayale Ahmed da kuma mataimakin shugaban majalisar dattawa suka fara don warware matsalolin.
Ya ce bukatun ASUU sun haɗa da biyan albashin da ya tsaya, alawus-alawus, da kuma sakin kudin farfaɗo da jami’o’i da aka amince da su tun bayan yarjejeniyar 2009 tsakanin ASUU da gwamnati.
Piwuna ya jaddada cewa idan gwamnati ta gaza cika waɗannan bukatu cikin wata ɗaya, ƙungiyar za ta koma yajin aiki ba tare da wani sabon gargadi ba.
Dalilin yajin aikin ASUU a 2025
Tun a ranar 12, Oktoba, 2025, ASUU ta ayyana yajin aikin gargadi na makonni biyu bayan karewar wa’adin kwanaki 14 da ta bai wa gwamnati tun daga 28, Satumba.
Ƙungiyar ta ce yajin aikin ya zama dole saboda kin biyan albashi da rashin bin yarjejeniyar 2009, da kuma rashin isasshen kulawa ga walwalar malamai da samar da abubuwan more rayuwa a jami’o’i.

Source: UGC
Sai dai gwamnatin tarayya ta soki yajin aikin, tana mai cewa tana kan aiki wajen warware matsalolin manyan makarantu.
Majalisar dattawa ta shiga tsakani
Punch ta wallafa cewa a makon da ya gabata, majalisar dattawa ta shiga tsakani domin rage zafin rikicin da ke tsakanin ASUU da gwamnati.
Shugaban kwamitin majalisar kan harkokin jami’o’i da TETFund, Sanata Aliyu Dandutse, ya bayyana cewa majalisar ta damu matuka da yadda gwamnati ke tafiyar da batun.
Ya kara da cewa majalisar za ta shiga tattaunawa kai tsaye da ASUU, ma’aikatar ilimi, da hukumar NUC don samar da sabuwar hanya mai dorewa wajen warware rikicin.
Barazanar da gwamnati ta yi wa ASUU
A wani rahoton, kun ji cewa ma’aikatar Ilimi ta fitar da wata takarda wacce ta umarci dukkan shugabannin jami’o’i su rika kirga malamai da suke aiki.
A cikin sanarwar, gwamnati ta ce tana da ikon aiwatar da dokar “ba aiki, ba biyan albashi.” a kan duk ma’aikacin da ya gaza zuwa wurin aiki yayin da ake yajin aiki.
Wannan matakin ya janyo suka jadaga bangaren malaman jami’a, wadanda suka ce hakan ba zai warware matsalar da ake ciki ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


