An Shiga Jimami bayan Masu Kwacen Waya Sun Hallaka Ma'aikaciyar Lafiya a Kaduna

An Shiga Jimami bayan Masu Kwacen Waya Sun Hallaka Ma'aikaciyar Lafiya a Kaduna

  • Ana zargin cewa wasu mutane masu kwacen waya sun hallaka wata ma'aikaciyar lafiya a garin Zariya da ke jihar Kaduna
  • Masu kwacen wayar dai sun yi sanadiyyar rasuwarta ne lokacin da suka yi yunkurin raba ta da wayarta a ranar Asabar
  • Mijin marigayiyar wanda ya suma saboda kaduwa, ya bayyana cewa alamu sun nuna an rotse mata kai ne yayin kwace wayar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Kwanan wata ma'aikaciyar jinya ya kare a hannun wasu da ake zargin masu kwacen waya ne a jihar Kaduna.

Ana zargin masu kwacen waya sun kashe wata ma’aikaciyar jinya mai suna, Hadiza Musa, a asibitin Gambo Sawaba da ke Zariya a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar ADC ta kori mataimakin shugaba da wasu manyan jami'ai 8, an fadi dalili

Masu kwacen waya sun kashe ma'aikaciyar lafiya a Zariya
Hadiza Musa da barayin waya suka kashe a Kaduna Hoto: Hamza Ibrahim Idris
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce mijin marigayiyar wanda yake aiki a Abuja mai suna, Hamza Ibrahim Idris, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Marigayiyar wadda masu kwacen wayar suka yi silar rasuwarta, ita ce mataimakiyar shugabar sashen haihuwa a asibitin Gambo Sawaba.

Yadda aka kashe malamar asibitin?

Hamza Ibrahim Idris ya bayyana cewa an kashe mai dakinsa ne a ranar Asabar yayin da take dawowa daga wajen aiki.

Ya ce ta kira shi a ranar Asabar ta sanar masa da cewa za ta je wajen gyaran gashi da shagon masu magani a filin Mallawa da ke kusa da Tudun Wada Zariya.

Kara karanta wannan

'Dan Najeriya ya yi amfani da kayan aikin mace, ya burma kansa a matsala a Ingila

Mijin ya bayyana cewa kiransu na karshe da ita bayan ya tura mata kudi shi ne lokacin da ta bar shagon maganin wajen karfe 6:00 na yamma, inda tun daga nan bai sake samun ta ba.

Ya ce ya ci gaba da kiran ta har zuwa safiyar ranar Lahadi amma ba ya samun ta, sai ya dauka cewa cajin wayarta ne ya kare.

Hamza Ibrahim Idris ya samu farfadowa daga sumar da ya yi a ranar Talata, sakamakon girgizar da ya yi bayan aukuwar lamarin.

Ya bayyana cewa daga baya ya gano matar ta sa ta hau babur din haya kusan ƙarfe 6:30 na yamma a ranar Asabar, amma daga bisani wasu mutane suka kai mata hari don su kwace wayarta.

An bugi marigayiyar a kai

Kara karanta wannan

Bayan murabus daga PDP, ministan Buhari na kokarin 'hana' gwamna shiga APC

Ya bayyana cewa yana zaton dukan da aka yi mata a kai wanda ya jawo jini ya taru, shi ne ya yi silar rasuwarta.

Masu kwacen waya sun yi kisa a Zariya
Hamza Ibrahim Idris tare da iyalansa Hoto: Hamza Ibrahim Idris
Source: Facebook

Hamza Ibrahim Idris ya ce bayan ta suma, sai barayin suka sace wayarta sannan suka jefar da ita a gefen titi kusa da filin Idi na Mallawa a Tudun Wada Zariya.

Hamza ya bayyana cewa rasuwarta na zuwa ne watanni uku bayan rasuwar ’yar uwarta, inda ta ɗauko ‘ya’yanta uku suka dawo wajen ta da zama.

Barayin waya sun kashe jami'in tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu masu kwacen waya sun hallaka wani babban jami'in soja a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Ana fargabar mutane da yawa sun mutu da wata tanka ta yi bindiga a Najeriya

Masu kwacen wayar sun hallaka jami'in sojan na ruwa ne mai suna Commodore M. Buba a Unguwar Kawo da ke karamar hukumar Kaduna ta Arewa.

Majiyoyi sun ce 'yan daban sun yi kokarin kwace wayarsa da sauran kayayyakin da ke hannunsa a kusa da gadar Kawo.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng