MTN zai Katse Sabis a Yankuna 101 a Kano da Wasu Jihohin Arewa 2

MTN zai Katse Sabis a Yankuna 101 a Kano da Wasu Jihohin Arewa 2

  • Kamfanin MTN ya bayyana cewa zai gudanar da aikin gyaran hanyar sadarwa a wasu jihohin Arewa a ranar 25 ga Oktoba, 2025
  • Aikin zai shafi wurare 101 a jihar Kano da wasu jihohi biyu kuma zai ɗauki sa'o'i biyu daga ƙarfe 6:00 na safe zuwa 8:00 na safe
  • MTN ya ce aikin na da nufin inganta tsarin sadarwa da ƙarfafa na'urori domin samar da sabis mai karfin gaske a jihohin da aka ambata

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Kamfanin sadarwa na MTN ya sanar da cewa zai gudanar da aikin gyaran hanyar sadarwa a sassan jihohin Kano, Borno da Adamawa a ranar Asabar, 25 ga Oktoba, 2025.

Kamfanin ya bayyana cewa aikin, wanda zai ɗauki tsawon awa biyu kacal daga ƙarfe 6:00 na safe zuwa 8:00 na safe, na iya haifar da katsewar sabis a wasu yankuna na jihohin uku.

Kara karanta wannan

Za a dauke wutar lantarki na kwanaki 10, an lissafa yankuna 25 da abin zai shafa

Ofishin MTN
Hoton wani ofishin kamfanin MTN. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Daily Trust ta ce MTN ya ce matakin wani ɓangare ne na shirinsa na ƙarfafa hanyar sadarwa da tabbatar da ingantaccen sabis ga abokan hulɗarsa a Arewacin Najeriya.

Dalilin gyaran da MTN zai yi a Arewa

Kamfanin ya bayyana cewa aikin zai haɗa da gyara a wani sabon layin igiyar sadarwa da aka mayar tsakanin AFCOT da kauyen Bawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a yi aikin ne domin sauya sassan da suka lalace da rage haɗuwar wayoyi masu yawa da ke kawo matsalar rashin ingancin hanyar sadarwa.

A cewar MTN, wannan mataki zai taimaka wajen rage matsalolin da ake fuskanta a baya tare da samar da ingantaccen tsarin sadarwa mai ɗorewa.

Wuraren da gyaran zai shafa a jihohi

Kamfanin ya ce aikin zai shafi yankuna 15 a cikin jihohin uku, inda suka haɗa da Nasarawa a jihar Kano.

Haka zalika zai shafi Girei, Song, Mubi ta Arewa, Hong, Gombi, Fufore, Mubi ta Kudu, Madagali, Michika, Maiha, da Yola ta Arewa a jihar Adamawa.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An gano masu yayata 'labarin kisan kiristoci' a Najeriya

A jihar Borno kuwa, rahotanni sun ce aikin zai shafi ƙananan hukumomin Chibok, Askira/Uba da Shani.

Ofishin MTN a Najeriya
Wani mutum na tafiya kusa da ofishin MTN a Najeriya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Business Day ta wallafa cewa kamfanin MTN ya bayyana cewa sabis ɗin 2G, 3G, 4G za su kasance ba su aiki a lokacin da ake gudanar da gyaran.

Bayanin MTN ga kwastomomin jihohin

Kamfanin ya bayyana cewa yana sane cewa za a iya samun tangarda a lokacin gyaran, amma ya nemi fahimtar kwastomomi tare da ba su haƙuri kan duk wata matsala da za ta taso.

Sanarwar kamfanin ta ce:

“MTN na bada haƙuri kan duk wata damuwa da wannan gyara zai iya haifarwa, tare da godiya ga kwastomomi bisa fahimtarsu.”

MTN ya yi magana kan farashin Data

A wani rahoton, kun ji cewa kamfanin MTN ya yi magana a lokacin da ya kara kudin Data a watan Fabrairun 2025.

A lokacin da ya kara kudi ba zato ba tsammani, 'yan Najeriya sun yi korafi a kafafen sadarwa suna cewa kudin ya yi yawa.

Biyo bayan korafin, kamfanin ya ba jama'a hakuri tare da cewa ya riga ya fitar da sabon farashi mai rahusa ga abokan hulda.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng