Damina ba Ta Kare ba: Ruwan Sama Zai Sauka a Taraba, Kogi da Wasu Jihohin Arewa
- NiMet ta yi hasashen cewa ruwan sama da iska mai karfi za su sauka a wasu sassan Najeriya ranar 22 ga Oktoba, 2025
- Hukumar ta yi gargadi ga direbobi da mazauna garuruwan da ke fuskantar ambaliya da su dauki matakan kariya da wuri
- NiMet ta kuma shawarci kamfanonin jiragen sama su nemi rahoton yanayi na daga gare ta don gujewa hadurran jirgi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar hasashen yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen ruwan sama da iska mai matsakaicin karfi a wasu sassan kasar a ranar Laraba, 22 ga Oktoba, 2025.
Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin rahotonta na yau da kullum da ta fitar a ranar Talata, inda ta shawarci jama’a su dauki matakan kariya don gujewa hadurran da ka iya tasowa.

Source: Original
Yiwuwar ruwan sama a jihohin Arewa
A cikin sanarwar da ta fitar a shafinta na X, NiMet ta rahoto cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Ana sa ran za a samu hasken rana mai dauke da dan hazo a safiyar Laraba, yayin da ake hasashen samun dan ruwan sama a kudancin Taraba.”
Hakan na nufin cewa yawancin jihohin Arewa za su fuskanci yanayi mai zafin rana da bushewar kasa, amma za a iya samun iska a wasu sassan jihohin.
A yankin Arewa ta Tsakiya kuwa, NiMet ta yi hasashen hasken rana da safe, sannan daga baya a sa mu iska da ruwan sama a wasu sassan Kogi, Kwara, Benue, Abuja, da Nasarawa.
Hukumar ta yi gargadin cewa ruwan sama na iya kawo hadari musamman ga hanyoyin mota da wuraren da ke da tarihin ambaliya.
Hasashen ruwan sama da iska a Kudu
NiMet ta kuma rahoto cewa:
“A yankin Kudu, ana sa ran samun hadari tare da ruwan sama da tsawa a wasu sassan Edo, Ogun, Ondo, Ebonyi, Cross River, Rivers, Lagos, da Akwa Ibom.”
Da yammacin ranar kuwa, NiMet ta ce akwai yiwuwar a samu iska mai dauke da ruwan sama mai matsakaicin kari a mafi yawan jihohin Kudu.
NiMet ta kuma yi gargadin cewa ruwan sama na iya jawo hadurra, tare da yiwuwar ambaliya a wasu wurare.

Source: Original
Muhimmancin bibiyar hasashen yanayi
Hukumar NiMet ta kara da cewa jama’a su ci gaba da bibiyar rahotonta na kullum don samun bayanai kan canjin yanayi da yadda za su kare kawunansu, inji rahoton Punch.
“Jama’a su ci gaba da bibiyar rahoton NiMet don samun bayanai cikin lokaci,” in ji hukumar.
NiMet dai tana karkashin ma’aikatar sufurin jiragen sama da harkokin sararin samaniya ta tarayya, inda take da alhakin bayar da hasashen yanayi, lura da yanayin ƙasa da isar da gargadin gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyi.
Malamai sun fita rokon ruwa a Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa, malaman Musulunci a Kano sun bukaci ɗaukacin al'umma su fita sallar rokon ruwa sakamakon ƙarancin ruwan da ake fama da shi.
Shugaban majalisar malamai ta Kano, Sheikh Ibrahim Khaleel ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rattaɓa wa hannu, aka raba wa manema labarai,
Sheikh Ibrahim Khaleel ya buƙaci musulmi su fito sallar rokon ruwa gobe Asabar da misalin ƙarfe 9:00 domin neman taimakon Allah a daminar bana.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


