Ta Yi Tsami tsakanin Fadar Shugaban Kasa, Kungiyar CAN kan Zargin Kisan Kiristoci
- Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta zargi Fadar Shugaban Kasa da yin karya kan tattaunawar da aka yi da Daniel Bwala
- Kungiyar ta ce rahoton da aka fitar ya cike yake da ƙarya da rashin hankali musamman kan zargin kisan Kiristoci a Najeriya
- CAN ta ce ba ta taɓa musanta cewa ana kashe Kiristoci ba, tana mai cewa fadar shugaban kasa ta juya hakikanin ma’anarta
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta zargi Fadar Shugaban Kasa da yin ƙarya da wuce gona da iri kan rahoton zargin kisan Kiristoci.
CAN ta bayyana cewa rahoton fadar shugaban kasa ya nuna kamar ta musanta cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya, abin da ta ce ƙarya ne kuma rashin mutunci.

Source: Twitter
Shugaban CAN, Rabaran Daniel Okoh, ya karyata hakan, yana cewa rahoton na neman juya gaskiya kuma yana kaskanar da wahalar da Kiristoci ke sha a faɗin ƙasar, cewar Punch.

Kara karanta wannan
Sarkin Musulmi ya nuna yatsa ga kasashen Yamma kan zargin kisan Kiristoci a Najeriya
Martanin Bwala kan zargin kisan Kiristoci
A wata hira da yan jarida, hadimin shugaban kasa, Daniel Bwala ya dage cewa babu wani kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Bwala ya ce rahoton da aka dogara da shi ya samo bayanai daga kafafen labarai da kungiyoyin sa-kai, waɗanda suka saka batun addini cikin binciken.
Sai dai Daniel Bwala ya dage cewa babu wani kisan kiyashi a Najeriya, yana mai cewa rahoton da aka ambata tsoho ne saboda ya shafe shekaru hudu.
Ya ce Musulmai da Kiristoci duka suna fuskantar hare-hare daga kungiyoyin ta’addanci kamar Boko Haram da ‘yan fashin daji a Arewa maso Yamma.

Source: Facebook
'Kisan' Kiristoci: CAN ta caccaki fadar shugaban kasa
Sai dai CAN ta ce a lokacin ganawar, ta bayyana cewa matsayinta kan kisan Kiristoci ya daɗe yana nan, kuma babu wani lokaci da ta rage a abin da ke faruwa.

Kara karanta wannan
Zargin kisan Kiristoci: An 'gano' yawan coci, masallatai da aka ruguza a Najeriya
Ta kara da cewa kalmar “kisan kiyashi” ta tozarta mutanen da suka rasa rayuka da gidaje sakamakon hare-hare.
Rabaran Mike Akpami ya gabatar da bayanai daga shafin www.orfa.africa, inda aka tabbatar da cewa ana kai hare-hare kan al’ummomin Kirista a sassa daban-daban na Afrika, ciki har da Najeriya.
Rahoton Vanguard ya ce CAN ta zargi Fadar Shugaban Kasa da ƙoƙarin rage tasirin binciken duniya ta hanyar karkatar da magana, tana mai cewa bai dace gwamnati ta yi wasa da irin wannan batu ba.
Kungiyar ta kuma bukaci gwamnati da jami’an tsaro su dauki mataki cikin gaggawa da adalci domin dakatar da kashe-kashe da gurfanar da masu laifi a gaban kuliya.
MURIC ta caccaki kungiyar CAN a Najeriya
Kun ji cewa kungiyar kare hakkin Musulmi ta MURIC ta yi magana kan zargin da ake yadawa kan cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya.
MURIC ta zargi shugabannin Kiristoci da amfani da Amurka wajen matsa wa gwamnati lamba domin nuna wariya ga Musulmai.
Shugaban kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola shi ya bayyana haka inda ya ce rahoton da wasu ke yadawa ba gaskiya ba ne.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng