Kana Naka: Darakta Ta Mutu a Hatsarin Mota Kwana 4 kafin Ritaya a Aikin Gwamnati

Kana Naka: Darakta Ta Mutu a Hatsarin Mota Kwana 4 kafin Ritaya a Aikin Gwamnati

  • Ma'aikatan jihar Lagos sun yi babban rashin wata darakta bayan faruwar mummunan hatsarin mota da ya afku wanda ya yi sanadinta
  • Jami’ar a hukumar LASRRA, Hajiya Serifat Olubukola Talabi, ta rasu kwana hudu kafin ritayarta da kuma zagayowar ranar haihuwarta
  • An ce motar da ke kan hanyar Lagas-Ibadan ce ta buge ta yayin da take kokarin ketare titi kusa da sansanin RCCG a Ibafo

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Lagos - An shiga jimami bayan sanar da rasuwar babbar darakta a wata hukuma a jihar Lagos bayan hatsarin mota da ya rutsa da ita a jihar Ogun.

Jami’a a Hukumar Rajistar Mazauna Jihar Legas (LASRRA), Hajiya Serifat Olubukola Talabi, ta rasu kwanaki hudu kacal kafin ritayarta.

An rashin darakta a Lagos kwanaki kadan kafin ritayarta
Taswirar jihar Lagos da ke Kudu maso Yammacin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Darakta a Lagos ta rasu bayan hatsarin mota

Rahoton Daily Trust ya tabbatar da faruwar haka inda ta ce marigayiyar tana daf da bikin zagayowar ranar haihuwarta shekaru 60.

Kara karanta wannan

Ana fargabar mutane da yawa sun mutu da wata tanka ta yi bindiga a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyi sun ce wata mota ce ta buge ta a kan hanyar Lagos-Ibadan a ranar 18 ga Oktoba, 2025, yayin da take kokarin ketare titi.

Lamarin ya faru ne kusa da sansanin cocin RCCG da ke Ibafo da ke Jihar Ogun wanda ya tayar da hankulan mutanen yankin.

Talabi, wacce ke matsayin Daraktar Siyan Kaya a LASRRA, ta riga ta fitar da katin gayyata don bikin godiya, ritaya da ranar haihuwa da aka shirya gudanarwa a ranar 22 ga Oktoba, 2025, a Ikeja, Lagos.

Wata darakta a Lagos ta rasu bayan gamuwa da hatsarin mota
Marigayiya Serifat yayin da take shirin bikin zagayowar ranar haihuwarta. Hoto: Adesiyan Adeola.
Source: Facebook

Hukumar LASRRA ta yi jimamin rashin Serifat

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na LASRRA, Basirat Lawal, ta fitar, hukumar ta bayyana bakin cikinta kan rasuwar.

Basirat ta ce dukkansu suna cikin firgici, ta fito ofis ranar Juma’a, an gama shiri don ritayarta a ranar 22 ga Oktoba.

Ta ce:

"Muna cikin firgici bayan samun wannan labari, ta zo ofis ranar Juma’a, kuma an gama dukkan shirye-shirye don ritayarta a ranar 22 ga Oktoba, 2025.

Kara karanta wannan

Budurwa ta kashe kanta ana shirin yi mata auren dole da abokin babanta

"Ya kamata ta yi ritaya tun a ranar 13 ga Oktoba, 2025, lokacin da ta cika shekaru 60, amma babban manajanmu, Mrs. Bilikiss Adebiyi-Abiola, ba ta nan, shi ya sa muka dage zuwa 22 ga Oktoba, 2025. Hukumar za ta halarci jana’izarta.”

Abokan aikin marigayiyar da dama sun yi jimamin rashinta musamman a wannan lokaci da take daf da yin ritaya da kuma bikin zagayowar ranar haihuwarta.

An bayyana cewa marigayiyar ta fara aiki da LASRRA a shekarar 2018 kuma ta zama darakta a wannan shekara ta 2025.

Tsohuwar minista a Najeriya ta rasu

Mun ba ku labarin cewa Najeriya ta sake yin babban rashi bayan sanar da rasuwar tsohuwar minista wacce ta rike mukamin wakiliyar Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna jimami kan rasuwar Joy Uche Angela Ogwu, tsohuwar Ministar Harkokin Waje ta Najeriya mai shekara 79.

Marigayiyar ta kasance wakiliyar Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya (UN) daga 2008 zuwa 2017, inda ta jagoranci Majalisar Tsaro ta UN sau biyu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.