Lauyoyi Sun Gano Kuskuren Kotu da Ta ba da Umarnin Aurar da Ƴan TikTok a Kano
- Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) ta ce akwai kuskure a hukuncin kotun Kano na tilasta auren wasu 'yan TikTok
- Shugaban NBA, Afam Osigwe (SAN), ya ce babu wata kotu a Najeriya da ke da ikon tilasta wa mutum balagagge yin aure
- NBA ta bukaci a soke hukuncin kotun, tana mai cewa hukuncin ya saba tsarin mulki da tauye ‘yancin 'yan TikTok din
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) ta bayyana rashin amincewa da wani rahoto da ke cewa wata kotun majistare a Kano ta ba da umarnin a aurar da wasu 'yan TikTok.
Legit Hausa ta rahoto cewa kotun ta ba hukumar Hisbah umarnin aurar da Idris Mai Wushirya da Basira Yar Guda, wadanda shahararrun 'yan TikTok ne, cikin kwanaki 60.

Source: Facebook
Shugaban NBA, Mazi Afam Osigwe (SAN), ya ce wannan umarni cin zarafi ne ga tsarin mulki da kuma amfani da ikon kotu fiye da kima, cewar sanarwar da Barisra Hamza Nuhu Dantani ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Ba hurumin kotu ba ne” – NBA
Mazi Afam Osigwe ya ce babu wata kotu a Najeriya da ke da ikon tilasta wa mutum aure, domin aure lamari ne na yarda tsakanin mutane biyu, da suka balaga.
“Aure ba zai taɓa zama hukunci, gyaran hali, ko hanyar ladabtarwa ta shari’a ba,” in ji Osigwe cikin sanarwar da ya fitar ranar Talata.
Kungiyar NBA ta bayyana cewa wannan umarni ya saba wa hakkin dan adam, musamman na ‘yancin kai, mutuncin dan adam, da sirrin rayuwa.
NBA ta bukaci a soke hukuncin kotun Kano
A cewar Osigwe, irin wannan hukunci na nuna rashin fahimtar iyakar ikon shari’a kuma yana rage amincewar jama’a ga tsarin kotu.
Ya gargadi kotuna da su guji zama wurin tilasta al’ada ko gyaran hali a tsakanin jama’a.
Kungiyar ta bukaci mahukuntan shari’a a Kano su sake duba wannan hukunci da ake zargin alkaliya Halima Wali ta yanke.
Osigwe ya ce irin wannan hukunci na iya zama barazana ga ‘yancin jama’a da kuma haifar da abin koyi mara kyau a gaba.

Source: Facebook
NBA ta kafa kwamitin sa ido kan lamarin
Shugaban NBA ya umurci kwamitin kare ‘yancin jama’a da kungiyar mata ta NBA su sa ido kan shari’ar don tabbatar da adalci.
A cewarsa, wannan mataki zai tabbatar da cewa an kare hakkokin Idris Mai Wushirya da 'Yar Guda din da abin ya shafa, tare da bin doka yadda ya dace.
Ya jaddada cewa ‘yancin mutum ya zabi wanda zai aura yana cikin hakkin dan adam da kundin tsarin mulki ya tabbatar da shi.
“Babu wata hukuma da ke da hurumin yi wa wani mutum auren tilas, kai tsaye ko a kaikaice, ko da kuwa kotu ce,” in ji Osigwe.
A karshe, kungiyar lauyoyin ta bayyana cewa ana amfani da doka ne ta zama jagora, ba wai a zama mai sanya ra’ayi, addini, ko matsin lamba ga al’umma ba.
'Yan Najeriya sun yi martani
A zantawar Legit Hausa da Babawo Tabare da ke Katsina, ya ce zai so a ce an zartar da hukuncin kotu na daura auren 'Yar Guda da Maiwushirya.

Kara karanta wannan
Nnamdi kanu: An gano abin da Buratai, gwamnoni da wasu manyan kasa za su fada a kotu
"Ni ina so a daura auren nan, mu ga ta karyar 'kontent,' domin na fahimci Maiwushirya yana amfani da yarinyar ne don cimma wata manufa ta sa.
"Ba zai yiwu ba, yarinyar da a kwanakin baya ka zo kana cin zarafinta, kana nuna cewa babu wanda zai iya aurenta, kuma yau ka dawo kana bidiyon auren bogi da ita."
Babawo Tabare ya roki hukumar Hisbah ta Kano da ta gaggauta auren Maiwushirya da 'Yar Guda, ko hakan zai zama izina ga 'yan baya.
Sadiya Khadi ta ce:
"Na tabbata zuwa yanzu ya shiga taitayinsa, ya fahimci cewa ya yi kuskure, ina fatan za a tambaye su idan suna son juna da gaske a yi aure, idan ba da gaske suke ba, to ka da a yi auren nan.
"Ka da a zo garin son aiwatar da doka, wata matsala ta biyo baya, don sha'anin auren dole wuya ne da shi, sai a zo a yi haihuwar guzuma."
'Yar Guda ta kafa sharadin auren Mai Wushirya
A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugaban hukumar Hisbah na Kano, Sheikh Aminu Daurawa ya ce 'Yar Guda ta kafa sharadi na auren Idris Mai Wushirya.
‘Yar Guda ta bayyana cewa ba za ta zauna a gidan haya ba bayan aure ko kuma tare da 'yan uwan Mai Wushirya, a cewar Sheikh Aminu Daurawa.
Hukumar Hisbah ta ce ita ma ba za ta shirya auren 'yan TikTok din ba har sai an samu yardar juna tsakanin ma’aurata domin guje wa auren dole.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


