Gwamna a Najeriya Zai Cafke Dukan Malaman Addini? Gwamnati Ta Yi Karin Haske

Gwamna a Najeriya Zai Cafke Dukan Malaman Addini? Gwamnati Ta Yi Karin Haske

  • Gwamnatin Anambra ta yi karin haske kan rade-radin cewa tana shirin kama wasu malaman addinin Kirista a jihar
  • Gwamna Charles Soludo ya karyata jita-jitar da ke cewa yana kokarin damke malaman addini, musamman Bishof-Bishof na Katolika
  • Kwamishinan yada labarai, Dr. Law Mefor, ya ce labarin karya ne da aka kirkira domin tayar da hankalin jama’a da bata sunan gwamnati

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Awka, Anambra - Gwamnatin jihar Anambra ta yi martani bayan yada jita-jita cewa tana shirin kama malaman addini bayan ta zarce.

Gwamnatin ta karyata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa Gwamna Chukwuma Soludo na shirin aikata hakan ga malaman addini, musamman Bishof-Bishof na Katolika.

Gwamna ya karyata shirin kama malaman addini a Anambra
Gwamnan jihar Anambra a Najeriya, Charles Cukwuma Soludo. Hoto: Prof. Charles Chukwuma Soludo.
Source: Facebook

Martanin gwamna kan rade-radin kama malamai

Kwamishinan yada labarai, Dr. Law Mefor, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da Punch ta samu inda ya ce kanzon kurege ne.

Kara karanta wannan

Kebbi: An ji gaskiyar zance kan batun jawo sojojin haya don yaki da 'yan bindiga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mefor ya ce labarin ba gaskiya ba ne, kuma an kirkire shi ne domin ta da hankalin jama’a da kawo rikici a jihar.

Kwamishinan ya kara da cewa gwamnati na girmama hakkokin kowa, ciki har da na malaman addini.

Ya kara da cewa Gwamna Soludo zai ci gaba da yakar bokaye da malaman karya da suke amfani da sunan addini wajen yaudara, tare da tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta hada kai da tarayya wajen yakar masu amfani da takardun bogi.

Sanarwar ta ce:

“Hankalin gwamnatin jihar Anambra ya karkata ga wani labari na karya da ake yadawa, wanda ke zargin cewa Gwamna Soludo na shirin kama Bishof-Bishof da Katolika bayan sake zabensa.
“Muna bayyanawa a fili cewa wannan rahoto karya ne, babu hujja, kuma mugun nufi ne kawai. Misali ne na yada bayanan karya domin ta da hankalin jama’a da lalata zaman lafiya.
“Wannan aikin ne na wasu ‘yan adawa marasa iko da ke dogaro da farfaganda saboda gazawar yakin neman zaben su; ya kamata su mayar da hankali kan gyara yakin neman zabensu.”

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta jero abubuwan da suka jawo karyewar farashin abinci warwas

Gwamna ya gargadi mutanen jiharsa kan yada jita-jita
Gwamna Soludo yayin da yake jawabi ga al;ummar yankinsa. Hoto: Hoto: Prof. Charles Chukwuma Soludo.
Source: Twitter

Tabbacin da gwamnati ta ba malaman addini

Gwamnatin ta ba da tabbacin cewa gwamnan yana da cikakken niyyar kare hakkin malaman addini da kuma tabbatar da yancinsu a jihar.

“Gwamnatin Anambra na tabbatar wa jama’a, musamman cocin Katolika, cewa Gwamna Soludo yana da cikakken niyyar kare hakkinsu da ‘yancinsu.
“Muna rokon ‘yan jihar Anambra su yi watsi da wannan labari na karya, kuma su tabbatar suna neman hujja mai inganci kafin su yada irin wadannan labaran da ke iya ta da fitina.”

- Cewar sanarwar

Gwamna Soludo ya magantu kan raba Najeriya

Mun ba ku labarin cewa gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya ce cigaban Igbo yana daga hadin kan Najeriya, ba raba kasa ba.

Soludo ya bayyana cewa ya goyi bayan tattaunawa cikin lumana amma ba ra’ayin ballewa a Najeriya da IPOB ke so ba.

Ya ce dokar zaman gida ta ranar Litinin da kungiyar IPOB ta kawo ta daina tasiri saboda tsaro ya inganta a jihar Anambra.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.