'Yan Sanda Sun Shiga batun Budurwar da Ta Kashe Kanta kan Auren Abokin Babanta

'Yan Sanda Sun Shiga batun Budurwar da Ta Kashe Kanta kan Auren Abokin Babanta

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta ce ta fara bincike kan jita-jitar wata budurwa da ta kashe kanta bayan an tilasta mata auren dattijo
  • Mai magana da yawun rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce kwamishinan ‘yan sanda ya umarci a gudanar da bincike mai zurfi
  • Rundunar ta gargadi jama’a da su guji yada bayanai ba tare da tabbatarwa ba domin kauce wa tayar da hankali kan halin da ake ciki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno – Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta ce ta kaddamar da bincike kan wani rahoto da ke yawo a kafafen sada zumunta kan wata budurwa da ta kashe kanta.

Legit Hausa ta rahoto cewa lamarin ya faru ne a ƙaramar hukumar Gubio bayan an ce an tilasta mata aure da wani abokin mahaifinta.

Kara karanta wannan

Bello Turji ya saki sama da mutum 100 a sabon shirin ajiye makami da daina yaki

Budurwar da ta kashe kanta
Hoton budurwar da aka ce ta kashe kanta a Borno kan auren dole. Hoto: Zagazola Makama
Source: Twitter

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa mai magana da yawun rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Maiduguri.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana bincike kan budurwar da ta kashe kanta

Daso ya bayyana cewa manufar binciken ita ce tabbatar da ainihin abin da ya faru da kuma gano ko labarin na gaskiya ne ko kuma rade-radi.

Ya ce rundunar za ta tabbatar da adalci da gaskiya ta hanyar binciken da zai kunshi dukkan sassan da abin ya shafa.

A cewarsa:

“Rundunar ‘yan sanda ta Borno za ta tabbatar da cewa an kare mutunci da ‘yancin kowane ɗan kasa, musamman wajen tabbatar da gaskiyar wannan rahoto.”

Gargadin yada bayanai ba tare da tabbaci ba

Mai magana da yawun rundunar ya yi kira ga jama’a da su guji yada bayanai ba tare da tabbatarwa ba, musamman a lamurra masu sarkakiya irin wannan.

Kara karanta wannan

Budurwa ta kashe kanta ana shirin yi mata auren dole da abokin babanta

Ya ce irin wannan dabi’a na iya haddasa rudani, fargaba, da kuma yada bayanan da ba su da tushe cikin al'umma.

Sufeton 'yan sandan Najeriya
Sufeton 'yan sandan Najeriya, IGP Kayode. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Daso ya kuma tunatar da jama’a cewa dokar yanar gizo ta 2015 ta tanadi hukunci ga duk wanda ya yada bayanai na ƙarya ko suka saɓa da gaskiya a intanet.

Legit ta tattauna da wata budurwa

A wani bangare, wata budurwa da ta nemi a ɓoye sunanta ta shaida cewa ita ma tana cikin irin wannan yanayi na matsin lamba daga iyayenta kan batun aure.

Ta ce:

“Na bi dukkan matakan da suka dace domin guje wa wannan aure amma abin ya ci tura. Mahaifina ma yanzu baya ɗaga wayata saboda kin amincewa da na yi.”

Budurwar ta yi kira ga iyaye da su daina tilasta ‘ya’yansu aure, domin hakan na iya jefa su cikin damuwa ko yin abin da bai dace ba.

Mai Wushirya zai auri 'Yar Guda

A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Aminu Daurawa ya yi karin haske kan batun auren dan Tiktok Mai Wushirya da 'Yar Guda.

Kara karanta wannan

Sojoji sun ceto mutanen da 'yan bindiga suka azabtar, wasu sun gaza tafiya

Hakan na zuwa ne bayan kotu ta umarci hukumar Hisbah a Kano ta daura musu aure kan tuhume-tuhume da aka musu.

Shugaban hukumar Hisbah ya bayyana cewa akwai sharuda da suka gindaya domin daura auren da ake son yi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng