Abin da Atiku Ya Ce wa Kwankwaso da Ya Cika Shekaru 69 a Duniya
- Tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya taya Rabiu Musa Kwankwaso murnar zagayowar ranar haihuwarsa
- A sakon taya murna da ya fitar a ranar Talata, Atiku ya yabawa jajircewar Kwankwaso wajen hidimar jama’a, ilimi da ci gaban ƙasa
- Mabiya shafin Atiku da dama sun tura sakonni da Kwankwaso, inda wasu su ka yi fatan zai zama shugaban kasa a zaben 2027
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya aika saƙon taya murna ga tsohon gwamnan jihar Kano, Saanat Rabiu Musa Kwankwaso.
A yau Talata ne jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Sanata Kwankwaso ke bikin murnar zagoyarsa ranar haihuwarsa, inda ya cika shekaru 69 a doron kasa.

Source: Facebook
A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya bayyana Kwankwaso a matsayin ɗan siyasa mai kishin ƙasa.
Atiku ya yabi Kwankwaso
A cikin sakon, Atiku ya yabi jajircewar Kwankwaso wajen ci gaban ilimi da hidimar jama’a, inda ya bayyana shi da cewa ya zama abin koyi a kasa,
Atiku ya ce:
"Ina taya ɗan’uwana, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, murnar cika shekara 69 a yau."
"Jajircewarka wajen hidimar jama’a, ilimi da cigaban ƙasa na cigaba da zaburar da al’umma da dama tun daga tsofaffi har zuwa matasa."
Ya ƙara da cewa:
"Ina taya ka da iyalai da abokanka da masu maka fatan alheri murnar zagayowar wannan rana, tare da addu’ar ka ci gaba da samun ƙoshin lafiya da nisan kwana a shekaru masu zuwa."
Jama'a sun taya Kwankwaso murna
Bayan saƙon Atiku, mabiya shafinsa sun taya Kwankwaso murnar zagayowar ranar haihuwar, inda suka bayyana godiya da fatan alheri ga rayuwarsa.
@Drelmoatiku ya ce:
"Tsarin ilimin kyauta da Kwankwaso ya aiwatar a Kano ya ƙara yawan ɗaliban makaranta sosai. Abin farin ciki ne ganin yana bin sawun Atiku a fannin ilimi. Barka da cika shekara 69 H.E. Kwankwaso – fatan farin ciki da nasara mai ɗorewa!"

Source: Facebook
@YusufELERUJA ya rubuta cewa:
"Barka da zagayowar ranar haihuwa RMK. Da a ce za ku haɗa kai da PO ku karɓo Najeriya a 2027."
@MichaelDab88084 ya yi fatan alheri, ya ce:
"Barka da ranar haihuwa, ranka ya daɗe. Fatan hikimarka za ta kawo sauyi ga talakawa."
@IsaiahAkin80716 kuwa ya ce:
"Barka da zagayowar ranar haihuwa shugabanmu mai zuwa. Allah ya ƙara maka lafiya da tsawon rai."
Tinubu ya aika sako ga Kwankwaso
A wani labarin, mun wallafa cewa Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya aika saƙo na musamman tare da taya murnar zagayowar ranar haihuwar Rabi'u Musa Kwankwaso.
Shugaban ƙasa, Tinubu ya ce irin tasirin Sanata Kwankwaso a Arewacin Najeriya, musamman a Kano, ya nuna yadda yake kaunar talakawa kuma ke kishin ci gaban al'umma.
Tinubu ya ƙara da cewa Kwankwaso ya bayar da gagarumar gudunmawa a fannoni da dama—daga lokacin da yake mataimakin kakakin majalisar wakilai har zuwa gwamna na jihar Kano.
Asali: Legit.ng


