EFCC Ta Kwato N500bn a Mulkin Tinubu, Shettima Ya Fadi inda Aka Kai Kudin
- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta samu nasarori masu tarin yawa a yakin da take yi a Najeriya
- Kashim Shettima ya bayyana cewa hukumar ta samu nasarar kwato biliyoyin kudi cikn shekara biyu na mulkin Shugaba Bola Tinubu
- Mataimakin shugaban kasan ya nuna cewa hukumar ta kuma samu nasarar gurfanar da dubunnan mutane a gaban kotu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana nasararorin da hukumar yaki da cin hanci ta EFCC ta samu a karkashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Kashim Shettima ya bayyana cewa EFCC ta samu nasarar tara dukiyar da ta kai Naira biliyan 500 cikin shekaru biyu da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi a kan mulki.

Source: Twitter
Tashar Channels tv ta ce Kashim Shettima ya bayyana hakan ne yayin bude taron bita da horas da alkalai karo na bakwai wanda EFCC da cibiyar NJI suka shirya a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mataimakin shugaban kasan ya wakilci Mai girma Bola Tinubu a wajen taron, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar da hakan.
Tinubu bai yi wa EFCC katsalandan
Kashim Shettima ya ce manufar gwamnatin Tinubu ta rashin tsoma baki a harkokin hukumomin yaki da rashawa ta taimaka wajen karfafa yaki da cin hanci da kuma inganta gaskiya a hukumomin gwamnati.
“A matsayin gwamnati, mun fifita gaskiya da rikon amana ta hanyar karfafa hukumomin yaki da rashawa da kuma ba su cikakken ’yanci wajen aiwatar da aikinsu yadda doka ta tanada."
- Kashim Shettima
Ya ce wannan yanayi na aiki cikin ’yanci ya bada damar samun ci gaba mai yawa cikin shekaru biyu da suka gabata.
“Misali, EFCC ta samu nasarar gurfanar da sama da mutum 7,000 a gaban kotu kan laifin rashawa kuma ta kwato kadarori da kudi fiye da Naira biliyan 500.”
- Kashim Shettima
Ina ake kai kudin da aka kwato?
Shettima ya kara da cewa kudin da aka kwato daga hannun barayin gwamnati ana mayar da su cikin tattalin arzikin kasa domin tallafa wa shirye-shiryen cigaba kamar bada lamuni ga dalibai da shirin bayar da rance ga ’yan kasa.
“Kudin da EFCC ta kwato daga aikata laifuffuka ana amfani da su wajen tallafawa muhimman shirye-shiryen jin kai, ciki har da bada lamuni ga dalibai da tsarin bashi ga masu karamin karfi."
- Kashim Shettima

Source: Facebook
Shugaba Tinubu bai kare 'yan siyasa
Ya kuma jaddada cewa gwamnatin Tinubu ba ta kare kowa daga bincike ko gurfanarwa.
“Babu wani mutum ko kungiya da za ta iya cewa wannan gwamnati na kare ’yan siyasa. Mun ba kotuna da hukumomin yaki da rashawa cikakken iko don su aiwatar da aikinsu cikin gaskiya da adalci."
- Kashim Shettima
EFCC ta gayyaci shugaban NAHCON
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar EFCC ta gayyaci shugaban hukumar kula da Alhazai ta kasa (NAHCON), Farfesa Saleh Abdullahi Usman.
Hukumar EFCC ta gayyaci shugaban na NAHCON ne bisa zargin karkatar da kudi da suka kai sama da Naira biliyan 50 da suka shafi shirye-shiryen aikin Hajjin 2025.

Kara karanta wannan
Bayan shan suka, gwamnatin Tinubu ta yi magana kan sakin Maryam Sanda da sauran masu laifi
Daga cikin kudin da ake zargi an karkatar akwai Naira biliyan 25 da aka kashe wajen biyan haya da gina tantuna a kasar Saudiyya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

