Mutuwa Ta Ratsa Gidan Sanata, Ya Rasa Dansa da Jikansa cikin Sa'o'i 48
- Tsohon gwamnan Benue, Samuel Ortom, ya yi ta’aziyya ga Sanata Abba Moro kan rashin dansa jikansa
- Samuel Ortom ya ce mutuwar guda biyu cikin kwanaki biyu abin takaici ne da kalmomi ba za su iya bayyanawa ba
- Ta'aziyyar tsohon gwamnan na zuwa ne bayan mutuwa ta dauki mutum biyu a cikin iyalan Sanata Abba Moro
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Benue - Tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya mika sakon ta’aziyya ga shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Abba Moro, kan rashin da aka samu a cikin iyalansa.
Samuel Ortom ya yi wa Sanata Abba Moro ta'aziyya ne bisa rasuwar ɗansa da jikansa cikin sa’o’i 48.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta ce Samuel Ortom ya yi ta'aziyyar ne cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Terver Akase, ya fitar a ranar Litinin, 20 ga watan Oktoban 2025.
Sanata Abba Moro ya rasa mutum 2
Sanata Abba Moro na wakiltar yankin Benue ta Kudu a majalisar dattawan Najeriya.
An ruwaito cewa ɗansa, Victor Moro, wanda ya dawo daga kasar Turkiyya bayan ya kammala karatunsa, ya rasu a mummunan hatsarin mota bayan dawowarsa gida domin yin aikin yi wa kasa hidima (NYSC).
Mutuwarsa ta faru ne kwana biyu bayan rasuwar jikan Sanata Abba Moro mai suna Abba Moro Jnr, wanda ke da kimanin shekaru 10 a duniya.
Samuel Ortom ya yi ta'aziyya
A cikin sakon ta’aziyyar da Ortom ya fitar, ya bayyana lamarin a matsayin mummunan bala’i mai matuƙar taɓa zuciya wanda kalmomi ba za su iya bayyana shi ba, rahoton Daily Post ya zo da zancen.
“Mutuwar Victor Moro, matashi mai cike da buri wanda ya kammala karatu a Turkiyya kuma ya dawo gida domin yi wa kasa hidima, amma rai ya yi halinsa cikin hatsarin mota, abin bakin ciki ne kwarai."

Kara karanta wannan
Jam'iyyar PDP da sakatarenta na ƙasa sun samu sabani kan takardar da aka aika wa INEC
- Samuel Ortom
Ya ce wannan masifa ba ta shafi iyalan Moro kaɗai ba, har ma ta jefa abokai, ’yan uwa da al’umma baki ɗaya cikin alhini, musamman wadanda suka san Sanata Moro a matsayin shugaba mai kishin jama’a.

Source: Facebook
“Wannan lokaci ne na matukar bakin ciki ga ɗan’uwana kuma abokina, Sanata Abba Moro. Ba kalmar da za ta iya kwantar da zuciyar uba da ya rasa ɗa da jikansa a lokaci ɗaya. Zuciyata tana tare da shi da duk iyalansa."
- Samuel Ortom
Tsohon gwamnan ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da Ya ba su karfin zuciya da hakuri don jure wannan babban rashi, Ya kuma jikan waɗanda suka rasu da rahamarsa.
Tsohon Sufeto Janar ya rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Sufeta Janar na rundunar 'yan sandan Najeriya, Solomon Ehigiator Arase, ya yi bankwana da duniya.
Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da rasuwar Solomon Ehigiator Arase, wanda shi ne Sufeto Janar na 18 cikin jerin mutanen da suka taba jan ragamarta Najeriya.
Hakazalika marigayin wanda ya rasu a asibitin Cedarcrest na babban birnin tarayya Abuja bayan wata gajeriyar rashin lafiya, ya taba taba rike shugabancin Hukumar kula da ayyukan yan sanda a Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

