Bayan kusan Shekaru 10, An Yanke Wa Wadanda Suka Kashe Malamin Jami'ar Kano Hukunci
- Kotu ta yanke wa mutum biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan kama su da laifin kisan malamin jami'ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano
- Alkalin kotun, Mai Shari'a Fatima Adamu ce ta yanke wannan hukunci a zaman yau Litinin, 20 ga watan Oktoba, 2025
- Mutanen da aka yanke wa hukuncin sun aikata kisan ne lokacin da suka kai hari gidan malamin a watan Yuni, 2016
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Bayan kusan shekaru 10, babbar kotun jihar Kano ta kama mutum biyu da hannu dumu-dumu a kisan malamin Jami'ar Yusuf Maitama Sule (tsohuwar Northwest University).

Kara karanta wannan
Kotu ta bada umarnin daura auren fitaccen dan TikTok da wada kan bidiyon da suka yi a Kano
Wadanda ake tuhumar sun aikata wannan danyen aiki na kisan kai ne tun shekarar 2016, lokacin da suka aikata laifin fashi da makami.

Source: Original
A rahoton da Leadership ta wallafa yau Litinin, babbar kotun ta yanke wa mutanen biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa kashe malamin jami'ar da ke karkashin gwamnatin Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotu ta yanke wa mutum 2 hukuncin kisa
Mutanen biyu da aka yanke wa hukuncin su ne Aliyu Hussaini daga unguwar Sheka Sabuwar Abuja Quarters da Amir Zakariyya daga Unguwar Malam Quarters, duka daga karamar hukumar Kumbotso.
Da take yanke hukunci a ranar Litinin, Mai Shari’a Fatima Adamu ta same su da laifuffuka uku, hada baki, fashi da makami, da kuma kisan kai.
Mai shari’ar ta ce
“Ayyukan waɗannan mutanen sun nuna rashin mutunta darajar rayuwar ɗan Adam gaba ɗaya.
"Saboda haka, na yanke musu hukuncin shekara biyar a kurkuku saboda haɗa baki, shekaru goma saboda fashi da makami ba tare da zaɓin tara ba, sannan kuma hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kisan kai. Allah Ya ji kansu.”
Yadda zaman shari'ar ta kaya a Kano
Tun farko dai lauyan gwamnati, Lamido Abba-Sorondinki, ya shaida wa kotu cewa mutanen biyu sun aikata laifin ne a ranar 11 ga Yuni, 2016.
Ya ce sun haɗa baki sun kai hari gidan Buhari Imam, malami a jami’ar da ke unguwar Sheka Sabuwar Abuja, suka sace wayarsa sannan suka caccaka masa wuka a ciki, cinyoyi, da bayansa, wanda hakan ya yi ajalinsa.
Gwamnati ta gabatar da shaida uku, ciki har da rahotan likitoci da hotunan mamacin, don tabbatar da laifin, kamar yadda jaridar Punch ta kawo.

Source: Getty Images
Duk da cewa masu laifin sun musanta zargin, kotu ta gamsu kuma ta tabbatar da laifin bisa shaidu masu karfi fiye da shakku.
Kotun ta bayyana cewa laifukan da mutanen biyu suka aikata sun sabawa Sashe na 97(1), 298(c), da 221(a) na Dokokin Laifuka na Jihar Kano.
Kotun koli ta fara zama kan mawakin Kano
A wani labarin, kun ji cewa Kotun Koli ta fara sauraron shari’ar batanci da ake tuhumar wani mawaki dan kano, Yahaya Sharif Aminu da taba mutuncin Annabi SAW.

Kara karanta wannan
Tuna baya: Lokacin da aka yi yunkurin kifar da gwamnatin Obasanjo a mulkin farar hula
Tun a shekarar 2020, Kotun Shari'ar Musulunci a Kano ta yanke wa mawakin hukuncin kisa, amma daga baya aka soke shi tare da umarnin sake sauraron karar.
Lauyoyin da suka daukaka kara domin kare wanda ake tuhuma sun bayyana cewa suna fatan hukuncin da kotun Koli za ta yanke zai takaita aiwatar da dokar shari’ar musulunci.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
